Abin Da Yasa Har Yanzu FG Ba Ta Tura Wa Ƴan Bindiga Jiragen Yaƙin Tucano Su Ragargaje Su Ba

Abin Da Yasa Har Yanzu FG Ba Ta Tura Wa Ƴan Bindiga Jiragen Yaƙin Tucano Su Ragargaje Su Ba

  • Fadar shugaban kasa ta ce kafin a turo jiragen sama na Tucano daga Amurka don yaki da ta’addancin da ke arewa maso yamma, sai an kiyaye dokokin yarjejeniyar siyayyar jiragen don gudun Najeriya ta bata sunanta a Amurka
  • Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin din Trust inda ya ce duk abinda ya faru shugaban kasa za a daura wa laifi
  • Ya ce a dokar siyar da Tucano, akwai hani akan kai farmaki ga wani yanki na fararen hula da makamin kare-dangi, idan ba haka ba Amurka ba za ta kara siyar maka da makamai ba kuma alakarku za ta baci

Fadar shugaban kasa ta ce kafin a tura jiragen saman Tucano da aka siya daga Amurka don kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, akwai yarjejeniyar siyayyar jiragen da wajibi sai Najeriya ta kiyaye, idan ba haka ba, sunanta zai baci a idon Amurka.

Kara karanta wannan

Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargitsa kasar nan

Garba Shehu, Kakakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Trust TV, Daily Trust ta ruwaito.

Abin Da Yasa Har Yanzu FG Ba Ta Tura Wa Ƴan Bindiga Jiragen Yaƙin Tucano Su Ragargaje Su Ba
Dalilin da yasa har yanzu FG ba ta tura jirage yaki zuwa Arewa maso Yamma, Fadar Shugaban Kasa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

A cewarsa ana kokarin gudun bacin sunan Buhari ne a idon Amurka

Kamar yadda ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An horar da sojoji. Amma za a daura laifi akan shugaban kasa ne idan wani abu ya biyo baya. Muna so idan ya sauki mulki ya koma Kaduna ko Daura don ya huta, amma ba za mu so ya tsaya gaban kotun masu laifi ta kasa da kasa ba, hakan ba dabara bane. Mu bar sojoji suyi ayyukansu na yaki da ta’addanci.
“Idan kana harkoki da kasashe kamar Amurka, sai ka kula da maganganun mutane, saboda suna tasiri a wurinsu. Eh tabbas sun siyar wa gwamnatin Najeriya da jiragen Tucano. Kuma sun kalli dokar da ta yi hani da amfani da makaman kare-dangi ga wani yanki na fararen hula, idan ba haka ba Amurka ba za ta sake siyar mana da makamai ba.

Kara karanta wannan

Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari

“Idan ba a manta ba, sai da Shugaba Buhari ya hau mulki sannan alakar Najeriya ta gyaru da Amurka har ta amince suka siyar mana da makaman.
“Kuma gaskiya ne, tun farko sojojin sama ba su iya amfani da jiragen a Arewa maso Yamma ba, har bayan nan sai da aka dauki lokaci kafin suka fara harba makamai na bangare ba na kare-dangi ba.”

Ya yi magana akan kokarin gwamnati na ceto wadanda ‘yan bindiga suka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Dangane da kokarin da gwamnati take yi don ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, National Mail Online ta nuna inda Shehu ya ce sojoji suna da bamabaman da zasu iya amfani da su wurin halaka ‘yan ta’adda. Amma suna son ceto wadanda suka sace shiyasa gwamnati ta hana su amfani da su amma ana ta kokari.

A cewarsa, an ci gaba da amfani da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna bayan harin yayin da jirgin sojoji na sama ya ke biye yana raka jirgin kasan.

Kara karanta wannan

Kawai ka bude gidajen yari kowa ya fito: Babban Lauya ga Buhari kan yafewa Nyame da Dariye

Ya ce an dakatar da harkokin jirgin kasan ne bayan harin na wani lokaci don kada a nuna halin ko in kula ga iyalan wadanda mummunan lamarin ya ritsa da su.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel