Peter Obi: Ya Zama Dole a Bar Kudu Maso Gabas Ta Mulki Najeriya a 2023
- Tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Peter Obi ya ce wajibi ne a bar yankin kudi maso gabas ta mulka Najeriya
- Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin inda ya ce hakan ne adalci, daidaito da kuma nuna girma da daraja ga yankin, don haka dole a dauki Ibo a ba shi mulki
- Ya yi wannan maganar ne a wani taro na wakilan jam’iyyar PDP daga Jihar Ogun da sauran kusoshin jam’iyyar a ofishin PDP da ke Abeokuta, Jihar Ogun
Jihar Ogun - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na PDP kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce dole ne a ba dan yankin kudu maso gabashin kasar nan mulkinta, Daily Trust ta ruwaito.
Ya tsaya akan cewa zaben shugaban kasa dan kabilar Ibo ne kadai adalci da kuma nuna girma ga yankin don haka wajibi ne a ba su dama.
Obi ya yi wannan maganar ne a ranar Litinin yayin wani taro da wakilan jam’iyyar na Jihar Ogun da sauran shugabannin jam’iyyar PDP a ofishinta da ke Abeokuta, Jihar Ogun.
Tsohon gwamnan ya bukaci wakilan da su kasance masu duba gaskiya, kada kudi ko son kai ya rinjaye su.
A cewarsa, yana nan akan bakarsa na burin daukaka Najeriya ta yadda duk wani dan kasar zai yi alfahari da ita.
Obi ya samu rakiyar Dr. Doyin Okupe, wanda ya ce duba da halin da Najeriya ta ke ciki, ya fi dacewa a tsayar da wanda aka san jajirtacce ne a matsayin shugaban kasa.
2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau
Ya koka akan rashin ayyuka ga matasa
Kamar yadda ya shaida bisa ruwayar The Punch:
“Ina mai tabbatar muku da burina na ganin ci gaban Najeriya. Kuma na kosa inga kasar nan ta zarce yadda take a halin yanzu.
“Abinda za mu ce shi ne a yi adalci da kuma daidaito, kuma a girmama junaye don mu ‘yan yankin kudu maso gabas mun ce muna bukatar shugabanci don sauya Najeriya.
“Babu kasar da ke da kaso 33 bisa dari na rashin aikin yi da kuma kaso 65 bisa dari na marasa ayyuka masu kyau da za ta ci gaba. Matasa da dama ba su da ayyukan yi.”
Ya ce mutanen kudu maso gabas ya dace a ba dama don su sauya kasar
Ya ci gaba da shaida yadda gwamnati ke rike da kudaden fanshon jama’an sannan makarantu da jami’o’i suke a kulle ba tare da kowa yana cewa komai ba.
Ya koka akan yadda yara da matasa suka koma shaye-shaye, don haka a cewarsa dole a sauya komai in har ana son ci gaba.
2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari
A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.
Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.
Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.
Asali: Legit.ng