Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

  • Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa Allah ya nuna masa cewa Atiku ne zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba
  • Atiku na neman takarar shugabancin Najeriya karo na shida bayan rashin samun nasara a lokutan baya
  • Da dama daga cikin mutane na yiwa dan siyasar wanda yake haifaffen jihar Adamawa kallon mai tsananin son mulki

Abuja - Tsohon dan majalisa wanda ya wakilci yankin Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, ya ce Allah ya fada masa cewa Atiku Abubakar ne zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

A ranar 23 ga watan Maris ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya ayyana aniyarsa ta shiga tseren shugabancin 2023 a hukumance a karkashin inuwar PDP.

Yan kwanaki bayan sanar da aniyarsa ta neman shugabancin kasar, kungiyar kasuwanci ta arewa maso gabas ta siya masa fom din takara na naira miliyan 40.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Sau uku Allah na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye
Sau uku Allah na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye Hoto: The Guardian

Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kamfanin sadarwa ta Daar, ya jagoranci wata tawaga don mika fom din a hedkwatar PDP da ke Abuja a ranar Litinin.

Da yake jawabi a yayin gabatar da fom din, Melaye ya bayyana Atiku a matsayin “dan Najeriya daya da ya zama dole mu nuna karfin gwiwa a kansa," rahoton The Cable.

Ya ce :

"Tsohon mataimakin shugaban kasar ya mallaki “fasahar gudanar da mulki da kuma ka’idojin siyasa.”
“Mun zo nan ne domin gabatar da fom din mutum daya tilo da zai hada kan tarayyar Najeriya.
“Mun zo nan ne don gabatar da fom din Ronaldo da Messi din PDP.
“Da ikon Allah, yayin da nake mika lasifika ga Cif Raymond Dokpesi domin gabatar da cikakken fom dinnan ga sakataren gudanarwa na kasa, ina so na bayyana cewa da yawa daga cikinmu idan muka yi kira ga Allah, Allah ba Ya kin amsa kiranmu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

“Idan muka kira shi, yana amsa kiranmu. Kuma ya kira ni sannan ya ce dani Dino, nace na’am ya Ubangiji na. ya sake kirana a karo na biyu, n ace na’am ya Ubangijina. Ya kira ni a karo na uku, sannan ya ce: “Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya.”

Shehu Sani, tsohon dan majalisa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya na cikin tawagar.

Atiku ne zai karɓi tutar takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Gwamna Fintiri

A gefe guda, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana kwarin guiwarsa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai lashe tutar takara ta PDP a zaɓen 2023.

Gwamna Fintiri wanda ya nuna tabbacin nasarar Atiku, ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a filin jirgin ƙasa da ƙasa na Yola da daren ranar Lahadi.

Tribune Online ta rahoto cewa wannan shi ne karo na farko da gwamnan ya koma cikin jiharsa tun bayan da Atiku ya ayyana shiga takara.

Kara karanta wannan

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya kamata ya gaji Buhari a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel