2023: Jonathan Ya Kamata Buhari Ya Miƙa Wa Mulki, In Ji Matasan Arewa
- Wata kungiyar matasan arewa mai suna 'Northern Youth Council' ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Goodluck Jonathan a 2023
- Kungiyar ta lissafa halaye na Goodluck Jonathan wanda hakan yasa ta ke ganin shine wanda kasar ke bukata domin dora wa kan abin da gwamnati yanzu ta yi
- Dr Abubakar, shugaban kungiyar na kasa ya ce ba wai baya goyon matasa su yi mulki bane amma idan aka duba jihohin da matasa ke gwamna za a ga ba abin da ake tsammani suka yi ba
Gabanin babban zaben shugaban kasa na 2023, wata kungiya mai suna 'Northern Youth Council' ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan saboda kwarewa, adalci, daidaita da cancanta, rahoton Vanguard.
Da ya ke magana a wani shiri a gidan talabijin na Arise TV, shugaban kungiyar, Dr Isah Abubakar ya ce mambobin kungiyar suna goyon bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya fi shugabannin duniya da dama kuruciya.
Dr Abubakar, wanda ya yaba wa kungiyoyi da dama masu neman tsohon shugaban kasar ya dawo Aso Rock a 2023 ya ce:
"Ina ganin babban basira ne a gayyaci tsohon shugaban kasar domin ya sake jagorantar harkokin kasar.
"Duba da cewa ya shugabanci Najeriya kimanin shekaru shida, mun yi imanin zai iya, yana da kwarewa da cancanta ya kai kasar mu mataki na gaba tare da dora wa kan abin da gwamnati na yanzu ta yi a bangaren ayyukan more rayuwa.
"Ba za mu iya musu cewa ana bukatar kwarewa a wurin mulkin kasa ba. A kasashen da ke da shugabanni masu shekaru 35 zuwa 40, dattawan sun riga sun dora kasar a kan turba da za ta iya tafiya ba tare da bukatar sa ido ba."
"Akwai jihohi a Najeriya da muke da gwamnoni masu kananan shekaru, kuma gaskiya abin da suke yi, ba mu yi tsammanin za su yi ba.
"Don haka ba zan ce bana goyon bayan matashi ya zama shugaban kasa ba, amma akwai alamar tambaya. Matasan da aka bawa dama su yi mulki, mene suka tsinana?," ya kara.
Dr Abubakar ya cigaba da cewa abin da muke bukata shine wanda zai mayar da mu yadda muke a baya lokacin da akwai hadin kai, ba mu tsani juna ba. Jonathan ya bamu wannan damar, ba ya rike mutane a zuciyarsa.
Ya kara da cewa Jonathan shine shugaban kasa a Afirka na farko da ya sha kaye a zabe kuma ya kira zababen shugaban kasa ya taya shi murna, don haka Najeriya na bukatar mutane masu hakuri kuma wadanda za su iya habbaka tattalin arziki yadda ya dace.
2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari
A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.
Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.
Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.
Asali: Legit.ng