Mu hadu a kotu: Gwamnan APC da mataimakinsa sun kalubalanci umarnin a tsige su

Mu hadu a kotu: Gwamnan APC da mataimakinsa sun kalubalanci umarnin a tsige su

  • Kotun daukaka kara ya karbi karar kalubalantar hukuncin da wata kotu ta yanke na tsige gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi da mataimakinsa, Kelechi Igwe
  • 'Yan siyasan biyu sun shigar da karar ne a sashin Abuja na kotun daukaka kara suna masu kalubalantar hukuncin da karamar kotun ta yanke
  • A cewar Umahi da Igwe, karamar kotun ta yi kuskure a tsarin doka kuma ta tafka karkatar da hukuncin da ta yanke a ranar Talata, 8 ga watan Maris akansu

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi da mataimakinsa, Kelechi Igwe, sun daukaka kara a ranar Talata, 8 ga watan Maris, bayan hukuncin da kotu ta yanke na tsige su daga mukamansu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnan da mataimakinsa a wata takardar daukaka kara da suka shigar a gaban kotun daukaka kara ta Abuja sun ce ba su amince da hukuncin da karamar kotu ta yanke akansu ba.

Kara karanta wannan

Kowawa APC: Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka

Gwamna Umahi ya tafi kotu
Mu hadu a kotu: Gwamnan APC da mataimakinsa sun kalubalanci umarnin tsige su | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

A cikin takardar karar mai lambar kara: FHC/ABJ/CS/920/2021, Umahi da Igwe sun lissafa dalilai takwas na daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke a jiya Talata, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Daya daga cikin dalilansu ya bayyana cewa kotun ta yi kuskure a dokance kuma ta bata a lokacin da ta ce babu wata hukuma da ta bayyana cewa idan gwamna ya fice daga jam’iyyar da aka zabe shi a cikinta ba zai iya shigar da karar jam’iyyar don dawo da aikinsa ba.

Takardar ta bayyana hujjoji da dalilai da suka sa yace sam ba wanda ya isa ya raba shi da kujerarsa ta mulkin jihar Ebonyi tare da mataimakinsa.

Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon ranar bakin ciki ga Abba Kyari yayin da ya bayyana a gaban kotu

A wani labarin, hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC tace har yanzun ba ta samu kwafin takardar hukuncin da babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yanke kan Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa ba.

Festus Okoye, Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin tara bayanai, ne ya faɗi haka yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Abuja.

Premium Times ta rahoto Mista Okoye na cewa INEC zata zauna kan lamarin da zaran ta karbi takardar hukuncin da Kotu ta yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.