Zaben 2023: CNG ta ce ta gano wani gwamnan APC, makiyin Arewa da dimokradiyya
- Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta bayyana rashin jin dadinta kan matsayar Gwamna Rotimi Akeredolu na dagewa kan dakile ‘yan takara daga yankin a zaben 2023
- A cewar CNG, lallai gwamnan na Ondo ya yi magana ne a matsayinsa na cikakken wanda ya ayyana kansa makiyin Arewa da dimokuradiyya
- Har ila yau, kungiyar ta lura cewa, Arewa ba za ta bari wasu daga Kudancin kasar su razana su ba, wadanda ke barazana a kullum, da zage-zage, da kuma yada kiyayya
Kalaman Gwamna Rotimi Akeredolu na cewa duk jam’iyyar siyasar da ta tsayar da ‘yan takarar Arewa gabanin zaben 2023, za ta fadi, ya jawo masa mummunan martani daga Arewacin kasar nan.
Da take mayar da martani kan batun na Akeredolu, Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) a ranar Laraba, 9 ga Fabrairu, ta yi ikirarin cewa shi makiyi ne ga tsarin dimokradiyya a kasar nan, inji wani rahoton Vanguard.
Kungiyar ta CNG ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman, a wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa kalaman gwamnan na Ondo barazana ce kawai, kuma hakan ba zai razana Arewa ta bar tsarin zabe da barin al’adar dimokuradiyya ba.
Kari kan haka, kungiyar ta bayyana cewa Akeredolu yana son amfani da matsayinsa wajen tauye ‘yancin ‘yan kasa na zaben ‘yan takarar da suke so da kuma damar ‘yan siyasa ta yin amfani da ‘yancinsu na tsayawa takara a zabe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, kungiyar ta bayyana Akeredolu a matsayin daya daga cikin wadanda suka ayyana kansu makiya Arewa da dimokradiyyar, wanda barazanarsu ba za ta tsinana komai ba.
Wani bangare na sanarwar CNG ya karanta:
“Domin kaucewa shakku, babu wata barazana da tsoratarwa daga Kudu da za su sauya tunanin ’yan Arewa game da tsarin tsayar da shiyya.
"Duk wani shugaban da za a zaba ya kamata a zabe shi ta hanyar dimokradiyya ba ta hanyar maganganun banza ba daga wani daga kowane yanki da kowane matsayi."
Kungiyar Arewa ta goyi bayan CNG
Da take goyan bayan matsayar CNG, kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta lura cewa Akeredolu ya kamata ya san abin da ya dace kuma ya bayyana batunsa daidai da abin da ke cikin kundin tsarin mulki kawai.
A cikin rahoton da Punch ta fitar, an ruwaito ACCF na cewa:
“A matsayinsa na babban lauya, ya kamata Gwamna Akeredolu ya san tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.
"Don haka, ba zai yiwu wasu gungun jihohi su taru su ce dole ne mu samar da shugaban kasa ba. Duk wanda ke hango wannan kujera dole ne ya ratsa kasar nan, Arewa da Kudu don biyan bukatun tsarin mulki.”
Rikici: APC da Buhari sun nemi a yi watsi da karar da ke neman tsige Buhari a daura Atiku
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar na neman soke zabensa tare da rantsar da tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar Atiku a matsayin shugaban kasa.
Wata kungiyar farar hula mai suna Civil Society Observatory for Constitutional and Legal Compliance (CSOCLC) ne ta shigar da kara, inda ta bayyana cewa takardar rantsuwar kotu da shugaba Buhari ya gabatar a zaben 2019 ta karya ce, inji rahoton Daily Trust.
CSO, ta bakin lauyanta, Nnamdi Ahaiwe Esq., ta bayyana cewa takardar rantsuwar kotu da shugaba Buhari ya yi a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2014, a babban kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja cewa:
Asali: Legit.ng