Sauya sheka: Yari da Marafa sun gana da Atiku da Saraki

Sauya sheka: Yari da Marafa sun gana da Atiku da Saraki

  • Ana rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa na iya sauya sheka daga jam'iyya APC a koyaushe
  • Manyan jiga-jigan na jam'iyya mai mulki sun gana da Atiku Abubakar da Bukola Saraki a ranar Alhamis
  • Rikici dai ya fara ne tun daga lokacin da uwar jam'iyya ta mika shugabancin APC a Zamfara a hannun Gwamna Bello Matawalle bayan ya sauya sheka daga PDP

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya yi wata ganawa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Alhamis, 27 ga watan Janairu.

Hakazalika Sanata Kabiru Marawan wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas ma ya kasance a cikin ganawar, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

A yanzu haka, Yari da Marafa suna wakiltan tsagi biyu mabanbanta a jam'iyyar APC reshen Zamfara.

APC na fuskantar gagarumin sauya sheka yayin da Yari, Marafa suka gana da Atiku da Saraki
APC na fuskantar gagarumin sauya sheka yayin da Yari, Marafa suka gana da Atiku da Saraki Hoto: newsday.com.ng
Asali: UGC

Atiku da Saraki suna cikin mutane takwas da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Koda dai babu cikakken bayani kan ganawar wacce ta gudana a gidan Saraki da ke Maitama Abuja, majiyoyi sunce hakan baya iya rasa nasaba da rade-radin sauya shekar manyan jiga-jigan na APC biyu.

The Nation ta kuma rahoto cewa a yan makonni da suka gabata, shugabannin na APC biyu sun ganawa makamanciyar hakan da Saraki, wanda daga bisani Marafa ya ce tattaunawa ce kawai ta zamantakewa.

Yari da Marafa suna ta samun sabani da shugabancin jam'iyyar APC a baya-bayan nan.

Rikicin ya samo asali ne daga hukuncin uwar jam'iyya na mika shugabancin jam'iyyar a Zamfara a hannun Gwamna Bello Matawalle bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar mai mulki a farkon 2021.

Kara karanta wannan

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

The Zamfara ex- governor and ex- senator have rejected Matawalle as leader of the APC in Zamfara.

Don haka sai tsohon gwamnan na Zamfara da tsohon sanatan suka yi watsi da Matawalle a matsayin shugaban APC a Zamfara. Harma ta kai suka kafa tsaginsu da suke shugabanta.

A yanzu haka, Yari na daya daga cikin yan takarar da ke neman shugabancin APC na kasa.

Sai dai, majiyoyi a jam'iyyar mai mulki sun ce da wuya ya zama shugaban, domin bai da goyon baya kamar na sauran masu neman kujerar.

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

A wani labari nadaban, mataimakin shugaban kungiyar matasan jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a arewa maso gabas, Mohammed Abdul Babangida, tare da sauran magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All progressive Congress (APC) a jihar Yobe.

Da yake zantawa da Leadership jim kadan bayan sauya shekar, Hon Babangida, ya ce tunda jam'iyyar ta yi watsi da su, sai suka yanke shawarar komawa karkashin inuwar APC mai mulki bayan tuntuba tare da sauran tsoffin mambobinsa na PDP a jihar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan Hanifa, an sake kashe wata yarinya a jihar Kano: Gwamna Ganduje

Babangida Yadi wanda ya fito daga karamar hukuma daya da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa nasarorin da APC ta samu a dukkan matakai sune suka ja hankalinsa da sauran wadanda suka sauya shekar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel