Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

  • Mataimakin shugaban kungiyar kamfen din Atiku a arewa maso gabas, Mohammed Abdul Babangida, ya sauya sheka zuwa APC tare da magoya bayansa
  • Babangida ya ce sun yanke hukuncin barin PDP ne saboda ta yi watsi da su
  • Ya kuma ce ci gaban da APC ta samu a dukkan matakai shine ya kwadaita masu komawa cikinta

Yobe - Mataimakin shugaban kungiyar matasan jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a arewa maso gabas, Mohammed Abdul Babangida, tare da sauran magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All progressive Congress (APC) a jihar Yobe.

Da yake zantawa da Leadership jim kadan bayan sauya shekar, Hon Babangida, ya ce tunda jam'iyyar ta yi watsi da su, sai suka yanke shawarar komawa karkashin inuwar APC mai mulki bayan tuntuba tare da sauran tsoffin mambobinsa na PDP a jihar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC
Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Babangida Yadi wanda ya fito daga karamar hukuma daya da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa nasarorin da APC ta samu a dukkan matakai sune suka ja hankalinsa da sauran wadanda suka sauya shekar.

A cewarsa, sun ji dadin irin nasarorin da jam’iyya mai mulki ta samu a dukkan matakan gwamnati, inda ya ce a shirye suke su jajirce don ganin nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Da yake magana a yayin bikin tarban nasu, shugaban jam'iyyar APC a jihar, Alhaji Mohammed Gadaka, ya basu tabbacin cewa ba za su yi karo da matsalolin da suka fuskanta a PDP a cikin sabon gidansu ba.

Leadership ta kuma rahoto cewa Gadaka ya shawarci masu biyayya ga jam'iyyar da wadanda suka sauya sheka da su mutunta matakai da ra'ayin jam'iyyar sannan su kuma yi aiki don nasararta a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

Ya bukaci mambobin APC da su ci gaba da ba Gwamna Mai Mala Buni goyon baya domin kai jihar gaba.

Bikin sauya sheka: Dan majalisan APC ya tsallake, ya koma tsagin adawa ta PDP

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mamba a majalisar wakilai, Yahaya Fatuba daga jihar Gombe ya bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Wata wasika da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya karanto a zauren majalisar ta nakalto dan majalisar yana cewa rikice-rikicen cikin gida da ya dabaibaiye jam'iyyar ne ya sa shi barinta.

A cikin wasikar, Fatuba ya bayyana cewa APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jihar Gombe, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel