Jam'iyyar PDP ta magantu kan wanda zata baiwa takarar shugaban ƙasa a 2023

Jam'iyyar PDP ta magantu kan wanda zata baiwa takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Wasu jiga-jigan PDP da kuma dai-daikun yan Najeriya na cigaba da yaɗa hasashen su kan yankin da jam'iyya zata baiwa takara
  • Sai dai PDP ta share tantama, yayin da ta bayyana cewa ba ta kai tikitin takarar shugaban kasa wani yanki ba a Najeriya
  • Kakakin jam'iyyar, Debo Ologunagba, ya gargaɗi masu yaɗa jita-jita mara tushe, su gaggauta dakatar da aikinnsu

Abuja - Jam'iyyar PDP ta musanta raɗe-raɗin cewa ta yanke ɗan yankin da zata baiwa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen dake tafe 2023.

Daily Trust ta rahoto babbar jam'iyyar hammaya na cewa har yanzun ba ta kai tikitin takara zuwa wani yanki ba a Najeriya.

Kakakin jam'iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, shine ya bayyana haka yayin da yake musanta jita-jitar da wasu ke yaɗawa.

Kara karanta wannan

Muazu Babangida Makaryaci ne, bamu yiwa Arewa alkawarin tikitin kujeran Shugaban kasa ba, PDP

Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PDP ta magantu kan wanda zata baiwa takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto shi yace:

"An jawo hankalin PDP kan kalaman wasu ɗai-ɗaikun mutane da jita-jita dake ikirarin cewa jam'iyyar mu ta miƙa tikitin takara ga wani yankin ƙasar nan."
"Kwata-kwata labarin bai kama da gaskiya ba domin bai fito daga jam'iyyar PDP ba. Domin kore tantama, PDP na son sanar da yan Najeriya cewa ba ta kai takara kowane yanki ba."

Meyasa ake ta wannan jita-jita?

Kakakin PDP ya kara da cewa tun farko an kafa PDP a kan tubalin demokaradiyya, wanda ya haɗa da tsarin mulkin karba-karba.

Sai dai a cewarsa kafin ɗaukan kowane mataki, wajibi ne sai an nemi shawari, tatauna wa da kuma diba a abubuwan da ake fuskanta da bukatar yan ƙasa.

"Saboda haka, PDP na rokon yan Najeriya, Mambobi da magoya baya su watsar da duk wata jita-jita da ikirarin baiwa wani takara ko yanki."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Fusatattun Mambobin APC sun maka uwar jam'iyya da Gwamna Buni a gaban Kotu

Daga nan kuma, Mista Ologunagba, ya miƙa godiyar jam'iyyarsa ta PDP ga yan Najeriya bisa soyayyar da suke nuna mata na jam'iyyar da zata ceto Najeriya kuma ta sake gina ƙasa.

A wani labarin na daban kuma Mambobin jam'iyyar PDP 4,000 zasu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jigawa

Jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa dake Arewa maso yammacin kasar nan tace nan ba da jimawa ba zata karbi mambobin PDP 4,000.

Shugaban APC a Jigawa, Sani Gumel, yace masu sauya shekan sun ɗauki matakin dawowa APC ne saboda kyakkyawan jagoranci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel