Da dumi-dumi: Majalisar dokokin Imo ta tsige wasu ‘yan majalisa 3 saboda dalilai

Da dumi-dumi: Majalisar dokokin Imo ta tsige wasu ‘yan majalisa 3 saboda dalilai

  • Majalisar dokokin jihar Imo ta tsige wasu 'yan majalisu saboda kin halartar zaman majalisa na tsawon lokaci
  • Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta yi alkawarin duba kasafin kudin jihar amma 'yan majalisar suka ki zuwa halartar zama
  • An samu hargitsi daga mabiyan wadanda aka tsigen, sun kuma ce lallai za su runtuma zanga-zangar adawa da hakan

Jihar Imo - A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Imo ta tsigewasu ‘yan majalisar dokokin jihar guda uku, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Tsigewar ta faru ne a farfajiyar majalisar bayan sanarwar da kakakin majalisar, Kennedy Ibeh ya bayar.

Taswirar jihar Imo
Da dumi-dumi: Majalisar dokokin Imo ta tsige wasu ‘yan majalisa 3 saboda dalilai | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

‘Yan majalisar da aka tsigen sun hada da Arthur Egwim (Ideato ta Arewa) Ngozie Obiefule (Isu) da Obinna Okwara (Nkwerre).

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Dalilin da aka bayar shi ne, a lokacin da:

“Gwamna ya gabatar da kasafin kudin 2022, majalisar ta yi alkawarin duba shi cikin hanzari. Wadannan ‘yan majalisar sun yi biris da halartar zaman majalisar wannan yasa shugaban majalisar ya fusata da hakan , don haka aka tsige su.”

Dangane da ayyana kujerar dan majalisa mai wakiltar Ngor Okpala, Tochi Okere, cewa za a iya neman mai maye gurbin ta, majalisar ta bayyana hujja da cewa:

“Ya shafe fiye da kashi daya bisa uku na zaman majalisar a cikin shekara guda bai zo ba kuma hakan yasa aka ayyana kujerarsa cewa babu kowa akanta kuma aka ayyana zabe zai gudana nan da kwanaki 90 masu zuwa.”

Sai dai hargitsi ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Imo, yayin da magoya bayan ‘yan majalisar da aka tsige daga mazabu daban-daban suka ce za su yi zanga-zangar nuna adawa da tsige wakilansu a zauren majalisar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel