Kano: Ilimin Addinin Musulunci Ka Ke Buƙata Ba Boko Ba, Tsohon Kwamishina Ya Faɗa Wa Ganduje

Kano: Ilimin Addinin Musulunci Ka Ke Buƙata Ba Boko Ba, Tsohon Kwamishina Ya Faɗa Wa Ganduje

  • Injiniya Muazu Magaji, tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano, ya shawarci gwamna Abdullahi Umar Ganduje
  • Bisa shawarar Magaji, kamata ya yi Ganduje ya bazama neman ilimin addini ba ya garzaya Jami’ar Harvard ba, don neman karin ilimi
  • Dama an samu bayanai akan yadda Ganduje ya bazama jami’ar da ke Amurka don halartar taro akan ilimin ingantaccen shugabanci na mako guda

Kano - Injiniya Muazu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, ya shawarci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan komawa don karo ilimin addini maimakon tafiya jami’ar Harvard don karo ilimi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Ganduje ya tafi Amurka don halartar wani taron kwas na sati daya “Bunkasa Shugabanci ” a Jami’ar Harvard da ke Boston.

Bayan samun wannan labarin ne tsohon kwamishinan ya lallaba shafinsa na Facebook inda ya ba gwamnan shawara, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Ilimin addinin musulunci ka ke buƙata ba boko ba, Tsohon Kwamishina ya faɗa wa Ganduje
Ilimin addinin musulunci ka ke bukata ba boko ba don jagorantar mu a Kano, Tsohon kwamishina ya fada wa Ganduje. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewarsa, gwamnan ya fi bukatar ilimin “Makarantar Allo” ma’ana ilimin addinin musulunci.

A cewar Magaji ilimomin bokon da Ganduje ya tara sun ishe shi

Magaji ya kwatanta horarwa akan ci gaban mulkin da Ganduje ya tafi Amurka don yi a matsayin abu mara amfani, ya ce digiri na farkon da ya yi a ABU da digirin digirgir din da ya yi a Ibadan sun ishe shi.

“Abinda ka fi bukata ne ba ka mayar da hankalinka a kai,” kamar yadda ya wallafa.

A cewarsa:

“Makarantar Allo ka fi bukata don sanin yadda za ka gudanar da ayyuka da kuma tattala dukiyar al’umma, ya kamata ka je don ka fahimci irin hadimai na kwarai da zaka dora don kulawa da fannoni daban-daban.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yabi Minista yayin da ya cika shekara 70, ya jinjinawa irin kokarinsa

“Ka nemi sani akan yadda Umar (RA) ya gudanar da mulkinsa don ba ma bukatar ka tafiyar da mu a irin hanyoyin Harvard.”

Ganduje ya tsige Magaji daga madafun iko a 2020

Dama a watan Afirilun 2020 ne Ganduje ya tsige Muazu Magaji akan kujerarsa sakamakon wasu maganganu da ya yi masu kama da murnar mutuwar marigayi Abba Kyari, shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammad Buhari.

Bayan wasu watanni, Ganduje ya kara mayar da Magaji a matsayin shugaban kwamitin harkar shigo da sinadarin Gas na NNPC/AKK a jihar Kano.

Sai dai, Ganduje ya kara tube Magaji daga kujerar inda ya zarge shi da rashin jajircewa akan ayyuka da iya shugabanci na kwarai.

Kano: Ganduje ya miƙa mulki ga mataimakinsa Gawuna, ya tafi Jami'ar Harvard

Tunda farko, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tafi kasar Amurka domin hallartar wani taro na sati guda a Jami'ar Harvard, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban ICPC ya tono kwangilolin da aka ba Sanatan APC, ya kai wa Buhari hujjoji

Sanarwar da kwamishinan Labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar ta ce Mr Ganduje zai hallarci taron 'Cigaban Jagoranci na Ainihi' a Tsangayar Koyar Dabarun Kasuwanci ta Harvard da ke Boston.

Ya ce gwamnan ya mika mulki tare da cikakken iko ga mataimakin gwamna, Nasir Gawuna, ya yi aiki a matsayin gwamna na wucin gadi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel