An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

  • Austin Braimoh ya roki Asiwaju Bola Tinubu ya ajiye batun zama shugaban Najeriya a zaben 2023
  • Braimoh yace ya kamata tsohon gwamnan na jihar Legas ya ci girma, ya bar wa mutanen Ibo takara
  • Ana ganin cewa babban jagoran na APC zai iya neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa

FCT Abuja - Yayin da aka fara yakin neman zaben 2023, shahararren ‘dan gwagwarmayar nan, Austin Braimoh ya ba jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu shawara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Austin Braimoh yana cewa ya kamata Asiwaju Bola Tinubu ya hakura da burin zama shugaban Najeriya, ya ba 'Yan Ibo dama.

Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021, Braimoh ya yi kira ga manyan jam’iyyun siyasa su kai tikitinsu zuwa kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yabi Minista yayin da ya cika shekara 70, ya jinjinawa irin kokarinsa

Mista Austin Braimoh yana ganin adalci da neman zaman lafiya shi ne jam’iyyun siyasa su mika tutar takarar shugaban kasar su ga wanda ya fito daga yankin Ibo.

“Arewa a dunkule ta ke shiyasa yanki daya zai iya fito da shugabannin kasa a jere, kuma ba za ayi wani rikici ba, amma babu irin wannan a Kudu.”
“Ina kira ayi watsi da ‘yan siyasan da suke bada shawarar ayi watsi da tsarin kama-kama, a daina la’akari da su a wajen neman mukami.” – Braimoh.
Bola Tinubu
Asiwaju Tinubu da Shugaba Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Jaridar tace Braimoh yace masu wannan ra’ayi ba su da adacli, kuma ba za samu zaman lafiya a haka ba.

“Ina kira ga jagoranmu, ubanmu, Bola Tinubu, na san ya na da hakuri, na san idan lokaci ya yi, zai fito yace ya janye takara, ya goyi bayan Ibo.” – Braimoh.

Kara karanta wannan

2023: Rikicin cikin gida zai kawo masa cikas a Kano, Tinubu zai zauna da Gwamna Ganduje

Haka aka yi a lokacin Obasanjo

Da yake bayani, Braimoh yace a 1998, manyan jam’iyyu sun yarda a bar Bayarabe ya zama shugaban kasa ne saboda abin da ya faru da MKO Abiola a 1992.

Mista Braimoh yace lokaci ya yi da Ibo za su rike madafan iko, ya na ganin duk wani yunkuri na hana ‘Yan kudu damar zama shugaban kasa, rashin adalci ne.

Rikicin APC a Kano

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi magana a kan rikicin cikin gidan APC, yace ba a kan titi ya tsinci siyasa ba, ya bada shawarar su rika hakuri da junansu.

Gwamna Ganduje yace ya fi shekaru 40 ya na siyasa, kuma ita ya karanta da yake jami'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel