Shugaban ICPC ya tono kwangilolin da aka ba Sanatan APC, ya kai wa Buhari hujjoji

Shugaban ICPC ya tono kwangilolin da aka ba Sanatan APC, ya kai wa Buhari hujjoji

  • Hukumar ICPC ta na zargin wasu ‘Yan majalisa da amfani da karfinsu wajen karbo kwangiloli masu tsoka
  • Daga cikin wadanda aka samu su na wawurar kudin gwamnati da sunan kwangila akwai Barau Jibrin
  • Sanatan na Kano ya yi amfani da kamfaninsa na Sinti Nig. Ltd, ya samu kwangiloli, amma ba ayi aikin ba

Abuja - Hukumar ICPC mai yaki da marasa gaskiya a Najeriya, ta gano yadda wasu ‘yan majalisa suka hada-kai da hukumomin gwamnati, suka karbi kwangiloli.

Jaridar Daily Nigerian tace binciken na ICPC ya fallasa yadda musamman Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin ya tashi da wasu kwangiloli na biliyoyin kudi.

Cikin kwangilolin da aka gano an ba Sanata Barau Jibrin akwai wani aiki da kamfanin Sinti Nig. Ltd ya samu, wanda ‘dan majalisar ne shugaban wannan kamfani.

Kara karanta wannan

Na janyo wa jama'ar Yesu abin kunya: Faston da aka kama ya yi garkuwa da Faston Katolika

Wannan bincike ya na kunshe a wani rahoto na “Constituency and Executive Tracking Exercise Phase 3 Report” da ICPC ta gabatarwa shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban ICPC, Bolaji Owasanoye da ya yi wannan bincike, yace wasu manya na amfani da kujerunsu wajen cin dukiyar kasa, maimakon taimakon al’umma.

Barau Jibrin Maliya
Shugaban kasa da Barau Jibrin Hoto: abdulbasi.abdulsamad
Asali: Facebook

Dabarar da masu iko su ke yi

"‘Yan majalisa da hadimansu ko manyan jami’ai suna amfani da karfinsu, su bada kwangiloli ga kamfanonin da suke da hannu a ciki ko wanda za su samu wani abu.”
“Ta tabbata da hujjoji cewa an saba dokar bada kwangiloli wajen wannan danyen aiki.” – ICPC.

Badakalar Sinti Nig. Ltd.

Rahoton yace a Nuwamban 2020, kamfanin Sinti Nig. Ltd na wani Sanata ya samu kwangilar kusan N200m na samar da kayan karatu a mazabar Kano ta Arewa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo

Sokoto Rima Basin Development Authority ta bada wannan kwangila na aikin da Jibrin Barau ya kawo. A ka’ida bai kamata a ba kamfanin Sanatan wannan aikin ba.

Binciken jaridar ya nuna ‘dan majalisar ne yake da mafi yawan hannun jarin Sinti Nig. Ltd. Sauran shugabannin kamfanonin ‘ya ‘yansa ne Zainab, Shawal da Khalil.

Wani korafi da aka kai wa EFCC ya nuna an ba kamfanin kwangilar N430 domin gina wuraren karatu. An dakatar da aikin, amma an gama biyan wadannan kudin.

Rikicin cikin gidajen APC

A wani rahoto da mu ka fitar a makon nan, kun ji jerin Gwamnoni da Jihohin da APC su ke fuskantar barazana a zaben 2023 mai zuwa a dalilin rikicin cikin gida.

Baya ga rigingimun Kano da Kwara, sai APC ta yi da gaske a wasu jihohin kudu. A Kano abin ya yi kamari tsakanin gwamna Abdullahi Ganduje da tsaginsu Barau Jibrin.

Kara karanta wannan

FG ta zargi ESN da yanka wasu ‘yan sanda tare da yada bidiyon gawarwakinsu a intanet

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel