PDP ta yi sabon shugaba: Jerin sabbin shugabannin PDP da aka zaba a taron gangami

PDP ta yi sabon shugaba: Jerin sabbin shugabannin PDP da aka zaba a taron gangami

A jiya Asabar 30 ga watan Oktoba ne jam'iyyar PDP ta gudanar da taron gangaminta, inda batutuwa da yawa suka fito daga jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci taron.

An kuma gudanar zaben shugabannin da za su rike manyan mukaman jam'iyyar a matakin kasa, inda aka sanar da zaben sabbin shugabannin jim kadan bayan kada kuri'u.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, an zabi tsohon shugaban majalisar dattawa, kuma dadadde a jam'iyyar PDP, Sanata Iyorchia Ayu.

PDP ta yo sabon shugaba: Jerin sabbin shugabannin PDP da aka zaba a taron gangami
Taron gangamin jam'iyyar PDP | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro sunaye da kujerun sabbin shugabannin da wakilan jam'iyyar ta PDP ta zaba.

Jerin sabbin shugabannin PDP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Deliget 3600 sun dira Abuja yayinda kotu ke shirin raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP

 1. Shugaban jam'iyyar PDP na kasa – Iyorchia Ayu
 2. Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa (Arewa) – Umar Damagum (Tare da abokin hamayya)
 3. Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa (Kudu) - Taofeek Arapaja (Tare da abokin hamayya)
 4. Sakataren PDP na kasa – Samuel Anyanwu (Ba hamayya)
 5. Ma'ajin PDP na Kasa - Ahmed Mohammed (Ba Hamayya)
 6. Sakataren tsare-tsare na kasa – Umar Bature (Ba hamayya)
 7. Sakataren kudi na Kasa - Daniel Woyegikuro (Ba hamayya)
 8. Shugabar Mata ta Kasa - Farfesa Stella Effah-Attoe (Ba hamayya)
 9. Shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa – Muhammed Suleiman (Tare da abokin hamayya)
 10. Mai ba da shawara kan harkokin shari'a – Kamaldeen Ajibade (Ba Hamayya)
 11. Sakataren yada labarai na Kasa – Debo Ologunagba (Ba a Hamayya)
 12. Babban mai binciken kudi na kasa – Okechuckwu Daniel (Ba hamayya)
 13. Mataimakin sakatare na kasa - Setoji Kosheodo (Ba Hamayya)
 14. Mataimakin ma'aji na kasa - Ndubisi David (Ba Hamayya)
 15. Mataimakin sakataren yada labarai na kasa – Ibrahim Abdullahi (Ba Hamayya)
 16. Mataimakin sakataren tsare-tsare na kasa – Ighoyota Amori (Ba Hamayya)
 17. Mataimakin sakataren kudi na kasa – Adamu Kamale (Ba hamayya)
 18. Mataimakiyar shugabar mata ta kasa – Hajara Wanka (Ba hamayya)
 19. Mataimakin shugaban matasa na kasa – Timothy Osadolor (Ba Hamayya)
 20. Mataimakin mai ba da shawara kan harkokin shari’a – Okechukwu Osuoha (Ba hamayya)
 21. Mataimakin mai binciken kudi na kasa – Abdulrahman Mohammed (Ba hamayya)

Read also

Jam'iyyar ZLP ta ruguje yayin da shugabanta da mambobi suka koma PDP

Fastocin neman tsayawa takarar kujerun siyasa daban-daban sun bayyana a filin taron gangamin PDP

A ranar taron gangamin, dandalin Eagle Square, wurin da ake gudanar da taron gangamin jam’iyyar adawa ta PDP, a halin yanzu yana cike da tutoci da fastocin talla daban-daban na ‘yan takarar siyasa.

Wasu daga cikin fastocin sun hada da na gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Hakazalika da tsohon dan sanata, Shehu Sani; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas; Doyin Okupe; Gwamna Aminu Tambuwal da sauran su.

Source: Legit.ng

Online view pixel