Sarkin Sheɗanu: Fitaccen Mai Maganin Gargajiya Na Najeriya Mai Mata 59 Da ƳaƳa Fiye Da 300 Ya Mutu

Sarkin Sheɗanu: Fitaccen Mai Maganin Gargajiya Na Najeriya Mai Mata 59 Da ƳaƳa Fiye Da 300 Ya Mutu

  • Mr Simon Odo, wani mai maganin gargajiya, wanda aka fi sani da ‘Sarkin shaidanu’ wanda ya auri mata 59 kuma yaransa sun kai 300 da jikoki da dama ya kwanta dama
  • Marigayi Odo, dan asalin Aji ne da ke karamar hukumar Igbo-Eze ta arewa da ke jihar Enugu ya mutu ne da safiyar Talata bayan ya yi kwarya-kwaryar jinya
  • Mr Emeka Oda, daya daga cikin yaransa ya sanar da mutuwar mahaifinsa ga manema labarai a gidansu inda ya ce ya mutu ne ya na da shekaru 74

Jihar Enugu - Mr Simon Odo, mai maganin gargajiya wanda ya auri mata 59 sannan ya na da yara 300 da jikoki da dama a jihar ya kwanta dama, The Nation ta ruwaito.

Marigayi Odo, dan asalin Aji ne da ke karamar hukumar Igbo-Eze ta arewa a jihar Enugu ya mutu ne da safiyar Talata bayan wani kwarya-kwaryar jinya da ya yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

Sarkin Sheɗanu: Fittacen Mai Maganin Gargajiya Na Najeriya Mai Mata 59 Da ƳaƳa Fiye Da 300 Ya Mutu
Fitaccen mai maganin gargajiya Simon Odo mai mata 59 ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Arise News
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Emeka Oda daya daga cikin yaran mamacin ne ya sanar da mutuwar ga wakilin NAN a gidansu inda ya ce ya mutu ne da shekaru 74.

Tuni aka fara shirye-shiryen birne shi

Odo ya ce an fara shirya yadda za a aiwatar da birniyar mahaifin nasu bisa wasiyyar da ya yi ga matansa da yaransa.

Dama kafin ya mutu ya bukaci idan ya mutu kada a ajiye gawarsa a ma’adanar gawawwaki, a yi hanzarin birne shi.

Kamar yadda ya shaida:

“Eh mahaifi na wanda aka fi sani da Sarkin Shaidanu ya mutu. Kuma ya rasu ne a ranar Talata da safe bayan ya yi ciwon makwanni uku.
“Mu na ta taron ‘yan uwa don tabbatar da mun birne shi cikin gaggawa ba tare da an kai gawarsa ma’adanar gawawwaki ba.”

Kara karanta wannan

Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC

Ya ce mahaifinsa mutum ne mai nuna musu kulawa da soyayya

Ya koka akan mutuwar mahaifinsu inda ya ce mutuwarsa ta yi matukar dukansu don shi uba ne mai nuna kauna da so ga iyalansa.

Ya kara da cewa:

“Tun safe abokan arzikinmu da mahaifinmu tare da masoya su ke ta yi mana ta’aziyya akan wannan mutuwar mai ban tsoro da girgizawa.”

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel