Mawakiya Ta Gaji da Gwauranta, Ta Amince Ta Zama Mata Ta 2 domin Kare Mutuncinta

Mawakiya Ta Gaji da Gwauranta, Ta Amince Ta Zama Mata Ta 2 domin Kare Mutuncinta

  • Fitacciyar mawakiya Tiwa Savage ta bayyana damuwar da ta shiga game da son aure a rayuwarta tana mai kaskantar da kanta
  • Mawakiyar ta ce tana iya amincewa ta zama mata ta biyu, idan hakan ne zai ba ta damar samun mijin kirki wanda zai kula da rayuwarta
  • Ta ce kasancewarta shahararriyar mace mai suna ya sanya ta da sauran mata wahala wajen samun abokin rayuwa nagari da kuma kwanciyar hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fitacciyar mawakiya a Najeriya, Tiwa Savage, ta yi magana kan aure da kuma damuwar da take ciki.

Tiwa Savage ta bayyana cewa tana iya amincewa ta zama mata ta biyu a gidan aure idan hakan ne hanyar da za ta samu mijin da zai girmama ta.

Mawakiya Tiwa Savage ta ce ta matsu ta yi aure
Fitacciyar mawakiya a Najeriya, Tiwa Savage. Hoto: @tiwasavage.
Source: Instagram

Ta bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da ita a 'Lip Service Podcast' da aka wallafa a bidiyon YouTube a jiya Juma'a 17 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Amnesty Int'l ta bukaci gwamnati ta soke hukuncin kisa a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Tiwa Savage ta yi aure a baya

Tun bayan fitowarta cikin shahararru a fagen waka, Tiwa Savage ta zama daya daga cikin fitattun mawaka mata a nahiyar Afirka.

Mawakiyar ta samu nasarori da dama da suka kai ta ga samun yabo da lambobin yabo daga sassan duniya baki ɗaya.

Ta yi aure da Tunji ‘TeeBillz’ Balogun a shekarar 2013, inda suka haifi ɗa ɗaya mai suna Jamal a 2015, sai dai suka rabu a shekarar 2018.

Tiwa Savage ta shirya zama mata ta 2
Mawakiya a Najeriya da ta lashe kyaututtuka da dama, Tiwa Savage. Hoto: @tiwasavage.
Source: Instagram

Wahalar da shahararrun mata ke sha da aure

Tiwa Savage ta tattauna kan wahalar da mata da suka shahara kuma suke da kudi ke fuskanta wajen samun abokin rayuwa nagari.

Mawakiyar mai shekara 44, ta bayyana cewa duk da nasarorin da ta samu a harkar waka, samun masoyin gaskiya ya zama abu mai wahala a gare ta.

Ta ce sau da yawa tana tsintar kanta a matsayin 'Sugar Mummy' watau mace mai daukar nauyin saurayinta, abin da ta ce bata so ya ci gaba.

Kara karanta wannan

Baya ta haihu: Akwai yiwuwar Tinubu ya janye afuwa ga wasu 'yan Najeriya

“Ina ji kamar ni 'sugar mama' ce, amma ban so hakan. Idan na hadu da mutum mai kyau da zai aure ni, yawanci ko dai yana da aure ko kuma yana cikin shekarunsa 50. Saboda haka ban sani ba, watakila na zama mata ta biyu. Ina ganin hakan zai yiwu."
“Zan iya zama da matar farko lafiya, saboda ba zan zama mai rigima ba. Zan ina fita yawon kide-kide, ba zan takura kowa ba, kuma zan girmama ta a matsayin matar farko.”

- Tiwa Savage

Tiwa Savage ta ce ta kusa makancewa

A baya, kun ji cewa shahararriyar mawakiya a Najeriya, Tiwa Savage ta bayyana yadda ta ke fuskantar matsalar makanta duk da kokarin kare hakan.

Savage ta ce ta shafe fiye da shekaru uku yanzu ta na fama da matsalar wacce ke neman hana ta gani karfi da yaji yayin da take kan ganiyarta a waka.

Mawakiyar ta fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a kafofin sadarwa inda ta ce da fama da matsala tana fargabar ka da ta makance.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.