Mutum Sama da 200,000 Sun Yanyame El Rufa'i, An Ragargaje Shi daga Shiga TikTok
- Kasa da awanni 24 bayan bude shafinsa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya samu mabiya sama da 200,000 a TikTok
- Tuni wasu daga cikin mabiyan su ka fara bayyana ra'ayinsu kan sauya sheka da ya yi daga jam'iyya mai muli ta APC zuwa SDP
- A hannu guda kuma, an samu masu adawar siyasa da ke zargin cewa tsohon gwamnan ya kasa boye dacin rasa kujerar minista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fara samun tambayoyi daban-daban, adawa, goyon baya da kuma zargi iri-iri a shafinsa na TikTok da ya bude kasa da awanni 24 baya.
Cikin awanni 24 kacal, shafin ya samu fiye da mabiya 200,000, yayin da bidiyon da ya wallafa na farko ya samu kallon sama da miliyan 1.9 tare da fiye da sharhi 21,000.

Kara karanta wannan
'Ku biyo ni TikTok': El-Rufai ya bude shafinsa, ya tara dubban mabiya cikin sa'o'i 24

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a cikin bidiyon, El-Rufa’i ya bayyana cewa burin shafinsa na TikTok shi ne ya rika bayyana ra’ayoyinsa kan siyasa da kuma sabuwar jam’iyyarsa ta SDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufa’i ya shiga TikTok daga barin APC
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fara amfani da TikTok ne kwanaki kadan bayan ya fice daga jam’iyyar APC kuma ya sauya sheka zuwa SDP.
Ya ce:
"Wannan shi ne kadai kuma sahihin shafina na TikTok. Ku shiga domin kallon bidiyo, sharhi da tattaunawa kan siyasar Najeriya da kuma ayyukan sabuwar jam’iyyarmu, SDP. Maraba da ku."
El-Rufa’i ya samu goyon baya a TikTok
Duk da cewa ba duk mabiya sama da 200,000 da suka fara bibiyar Nasir El-Rufa’i a TikTok ke goyon bayansa a siyasa ba, akwai daga cikinsu da ke yi masa fatan alheri.
Sarkirwa Mamman Titus ya ce:
"Ni daga Zangon Kataf nake, zan ci gaba da kaunarka, Mallam Nasiru El-Rufa’i, zan bi ka, Yallabai."
Ligali Basshiru Harmattan ya ce:
"Ni Bayarabe ne, amma na rantse, idan za ka yi mani alkawarin shugabanci nagari, zan bi ka."
Ycee ya ce:
"Zan ci gaba da girmama ka har abada saboda kyautar gida da ka yi wa mahaifina a lokacin da kake Ministan Abuja, sannan ka biya wa ‘yar uwata kudin makaranta."

Asali: Facebook
Aishayunusaadamu38 ta ce:
"Jama’a ku taho ga Mallam, Mallam mai dubun alheri, Mallam mai dubun nasara. Ina gwanin wani ga nawa! Tsakanina da kai sai addu’a. Allah Ya taimake ka da iyawarSa, Ya kare ka da kariyarSa."
Tiktok: Wasu sun zargi El-Rufa’i da cin amana
Yayin da wasu ke yi wa tsohon gwamnan fatan alheri a sabuwar jam’iyyarsa ta SDP, wasu daga cikin masu bibiyarsa sun zarge shi da zalunci a jihar Kaduna da kuma cin amanar Bola Tinubu.
Daga cikin masu yin tsokaci a karkashin bidiyon maraba a shafin, wasu sun zargi tsohon gwamnan da nuna fushinsa saboda Shugaban Kasa Bola Tinubu bai ba shi mukamin minista ba.
Daviez ya ce:
"Ka rasa tasirin da kake da shi a siyasa."
Daddy ya ce:
"Bayan ka shafe shekaru a kan mulki, ka yi mugunta kuma an samu kashe-kashe da dama a gwamnatinka. Yanzu lokaci ya wuce."
Mumin ya ce:
"Ka amince da alkawarin dan siyasa ne ka zalunci kanka."
Daga cikin mabiyan na sa kuma akwai 'yan ba ruwa na, wadanda ke tambaya a kan tsarin siyasar da tsohon gwamnan ya ke kai.
Zahraddeen na daga cikin irin wadannan mutane, kuma ya ce:
"Yallabai! Don Allah ka na son talaka? Amsa tsakani da Allah."
Ministan Tinubu ya soki El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa karamin Ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata ya caccaki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i bayan ya sauya sheka zuwa SDP.
A wata sanarwa da mai taimakawa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Seyi Olorunsola, ya fitar, an bayyana cewa El-Rufai yana kokarin raba kawunan ‘yan siyasa domin bukatarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng