"Ƙara Tsufa Kike Yi": Gwamna a Najeriya Ya Ba Ƴarsa Wa'adin Shekara 1 Ta Nemo Mijin Aure

"Ƙara Tsufa Kike Yi": Gwamna a Najeriya Ya Ba Ƴarsa Wa'adin Shekara 1 Ta Nemo Mijin Aure

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya gaji da ganin ƴarsa cikakkiyar budurwa babu aure har yanzu
  • Gwamnan ya ba ƴar tasa mai shekaru 28 wa'adin shekara daya da ta yi gaggawar fitar da mijin aure saboda tsufa take kara yi
  • Ƴar tasa mai suna Nike ita ta wallafa hirar tasu a shafinta na Instagram inda ta ce mahaifin nata ya matsu ta yi aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya shawarci ƴarsa kan yin aure tare da umartarta game da nemo miji.

Adeleke ya ba ƴarsa zukekiyar budurwa mai shekaru 28 wa'adin shekara daya da ta nemo mijin aure.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya fadi abin da ya dauke hankalin Abba a shekara 1 na mulki

Gwamna ya bukaci ƴarsa ta fito da mijin aure
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya ba ƴarsa wa'adin shekara 1 ta nemo mijin aure. Hoto: @nikos_babii.
Asali: Instagram

Osun: Gwamnan ya ce kullum tsufa yake

Ƴar gwamnan, Nike Ademola ta wallafa faifan bidiyon a shafinta na Instagram lokacin da gwamna ke ba ta shawara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwar ta tambayi mahaifinta cewa tana daf da cika shekaru 29 yaya yake ji har yanzu bata yi aure ba?.

Gwamnan ya amsa da cewa ya bata wa'adin shekara daya ta nemo miji saboda kullum kara tsufa take yi.

Nike ta tambayi mahaifinta kamar haka:

"Yanzu shekaru na 28 ina daf da shiga 29, yaya keke ji a ranka har yanzu ban yi aure ba?"

A martaninsa, gwamnan ya ce:

"Na baki wa'adin shekara daya kacal kiyi aure saboda kara tsufa kike yi ba kankancewa ba."

Osun: Shawarar Adeleke ga ƴarsa kan aure

Adeleke ya gargade ta da ta yi kokarin kawo miji a cikin wadanda suke nemanta a yanzu.

Kara karanta wannan

Mata 'Yar Najeriya ta koka bayan lauyar da ta sa mijinta ya saketa ta yi wuff da shi

"Ya kamata ki fara shirin aure yanzu, kina tsammanin baya kike komawa ne, ina son a cikin masu nemanki ki ce baba ga wanda zan aura."
"Kina sane da cewa shekara 28 na yi aure, har na haifi yayanki Adesina, yanzu kina shekaru 28, kiyi gaggawa fitar miji a cikin shekara daya."

Ademola Adeleke

Basarake ya bukaci ƴarsa ta nemo miji

Kun ji cewa babban Basarake a Najeriya, Oba Adeyeye Ogunwusi ya bukaci ƴarsa mai shekaru 30 da ta fito da mijin aure.

Sarkin ya bukaci hakan ne daga ƴar tasa bayan ganin ƴar ta kawo kai har tana neman tsufa a gidan iyayenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel