Bayan Dokar Hisba, Kyauta Dillaliya ta Tsunduma Aikin DJ

Bayan Dokar Hisba, Kyauta Dillaliya ta Tsunduma Aikin DJ

  • Shahararriyar 'yar fim din nan Fatima Nayo da aka fi sani da Kyauta dillaliya ta cikin shiri mai dogon zango na dadin kowa da ake haskawa a Arewa 24 ta tsunduma aikin DJ
  • Ta bayyana cewa ta shiga aikin kida a wurin taro wato DJ da sankira wato MC saboda ta lura babu mata da ke yiwa 'yan uwansu mata aikin yayin bukukuwa
  • Kyauta Dillaliya ta ce gadan-gadan ta fara aikin DJ bayan ta karbi shawarwari, kuma ba za ta daina fitowa a fina-finai ko ko kuma ta ajiye aikin MC, duka za ta hada

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta ji wuta, ta ba da tulin kyaututtuka ga ƴan mata 100 da za a aurar

Jihar Kano- Daya daga mata masu kidan zamani a bukukuwa, Fatima Nayo da aka fi sani da kyauta dillalaliya ta ce yanzu ta tsunduma aikin DJ da gaske.

Fatima wacce ta shahara a fim mai dogon zango na dadin kowa da ake nunawa a Arewa 24 ta ce yanzu za ta hada aikin sankira wato MC da DJ da fina-finai.

Fati Nayo Fulanin Asaline
Kyauta Dillaliya ta fada aikin DJ gadan-gadan Hoto: Fati Nayo Fulanin Asaline
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Kyauta Dillalaliya ta ce mata zalla za ta yiwa DJ a kokarinta na ganin an nishadantu yadda ya kamata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yadda na shiga aikin DJ,' Dillaliya

Fatima Nayo, wacce ta yi fice da sunan Kyauta Dillalaliya ta bayyana dalilinta na shiga aikin DJ, bayan hukumar hisba a jihar Kano ta dakatar da maza daga yiwa mata DJ

Ta ce ta lura da cewa mata na kiran maza DJ wajen taronsu, saboda haka ta shiga aikin.

Kara karanta wannan

"An yaudare ni": An fasa daura aure bayan ango ya gano amarya ta yi ciko a mazaunai

Daily News24 ta wallafa cewa haka Kyauta Dillalaliya ta ce wa'azin malamai na daga dalilin da ya sanya ta fara DJ.

"Bayan na yanke shawarar shiga harkar DJ sai na samu wani telana sunansa Mansur na nemi shawararsa a kan haka, inda ya karfafa min gwiwa cewa babu matsala."
"Sai na nemi ya raka ni Sabon Gari in sayo kayayyaki, amma ya ce min kamata ya yi in fara neman masu sana’ar sai in hada gwiwa da su don su koya min yadda harkar take sannan kuma na rika amfani da kayayyakinsu," a cewar DJ Dillaliya

Taron mata: Hisba ta hana maza DJ

A baya mun kawo muku labarin cewa hukumar hisba ta hana maza kida a wurin taron bikin mata a fadin jihar.

A sanarwar da ya fitar, babban kwamandan hisba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce daga yanzu mata ne kawai aka amince su yi kidan DJ a bikin mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel