Sadiya Marshall Ta Kunyata, Ta Janye Kalamanta Kan Layla da Ta Bar Hannun DSS
- Sadiya Marshall ta janye dukkanin maganganun da ta yi a yanar gizo game da Layla Ali Othman
- Kwanaki kusan biyar da aka ji ta fito a bidiyo tana wasu kalamai na cin mutunci da kuma bata suna
- A bidiyon da ya fito yanzu, Hajiya Sadiya Marshall ta zargi saurin fushi da jefa ta cikin nadama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A wani bidiyo da yake yawo a dandalin Facebook, Sadiya Marshall ta nuna tayi kuskure da ta saki bakinta kwanaki.
Kamar yadda ta furta da bakinta, tayi kuskure da tayi magana a yanar gizo ba tare da ta tuntubi Layla Ali Othman ba tukuna.
Sadiya Marshall ta ce mutum bai cika 10 ba
Sadiya Marshall ta ce a matsayinta na ‘yar adam maras cikakkiyar kamala, fushi ya jawo tayi abin da ya jawo tana nadama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sabon bidiyon, ta ce ta shafe kwanaki biyu tana neman yadda za tayi magana da Layla, da abin ya faskara sai ta ji haushi.
"Wannan bai kamata ba, wannan bai dace ba. Bai kamata mu bari fushi ya kai ga daukarmu har ta kai ga haka ba."
"Ya kamata mu ji kan magana tukuna, mu tsaya tukuna, ya kamata mu jira komai tsawon lokaci."
"Kuma wannan Baiwar Allah tayi aure ba a dade ba, bai kamata irin wannan ya faru ba."
- Sadiya Marshall
Sadiya Marshall tayi nadamar cin mutuncin Layla
A sabon jawabin da tayi wannan karo, Marshall ta ce ko da amaryar ‘dan majalisar ta kai shekaru 40, to ita ta girme ta.
Wani bidiyo ya nuna mai gidan ‘yar kasuwar ya kai maganar gaban DSS domin kare mutuncin matar da ya aura a bara.
Afuwar Sadiyar Marshall
"Ubangiji Allah ya ba ku hakuri, don Allah don Annabi kuyi hakuri. Ga dangina, don Allah ku yi hakuri."
"Ita ma na ba ta hakuri da danginta, don Allah kuyi hakuri. Kowa da kowa ya yi hakuri. A bar zage-zagen nan."
- Sadiya Marshall
A karshe ta bukaci jama’a su daina cin mutuncin kowa domin lamarin ya wuce, ta ce wannan bai tarbiyyar gidansu ba ce.
Martanin mutane a Facebook
Jama’a sun yi tir da danyen aikin da matar tayi, duk da ta fito karara ta nemi afuwar Layla Othman da duk wadanda abin ya shafa.
"Dokar Allah ta ce duk wanda ya jefi wani da fasikanci in bai kawo shaidu hudu ba sunansa maƙaryaci. A nan ya dace musulmi su tsaya. Amma saboda son yaɗa ɓarna ba ma iya bin dokar. Allah ya kyauta"
- Sheikh Dr. Kabir Asgar
"Da shari'ar musulunci ake a lanjeriya da sai an yi wa waccan matar hukuncin qazafi domin kar wani ma ya sake irin haka a nan gaba."
- Zahraddeen Idris Suleiman
A cewar Zahraddedn Suleiman akwai laifin wadanda su ka yi ta yada bidiyon, su ma hukuncin kazafi ya hau kan su domin suma su yiwa Laila sharri a fakaice.
Sadiyar Marshall v Layla Ali Othman
An ji yadda matar nan ta jefi Hajiya Layla Ali Othman da munanan zargi, daga ciki har da alfasha alhali tana da dakin miji.
Saboda haka Yusuf Gagdi ya nemi hukuma ta dauki mataki domin wanke iyalinsa.
Asali: Legit.ng