“Na Fi Da Yawa Daga Samarin Da Ke Neman Kulla Alaka Da Ni Kudi”, In Ji 'Yar Wasan Barkwanci Ashmusy

“Na Fi Da Yawa Daga Samarin Da Ke Neman Kulla Alaka Da Ni Kudi”, In Ji 'Yar Wasan Barkwanci Ashmusy

  • Fitacciyar 'yar wasan barkwanci Ashmusy ta ce ta fi da yawa daga samarin da ke tunkararta samun kuɗi
  • Ta ce wannan ne dalilin da ya sa har yanzu ba ta samu saurayin da za ta yi soyayya da shi ba
  • Ta kuma bayyana cewa tana son ta samu wanda ya fita samun kuɗi a duk wata ba wai wanda ta fi ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitacciyar 'yar wasan barkwanci Amarachi Amusi, ta yi magana a kan abinda ya hanata samun saurayin da za ta aura duk kuwa da yawan kuɗaɗen da take samu.

Ta bayyana hakan ne a yayin da ake zantawa da ita a cikin shararren shirin nan na ‘Tell Your Story’ da ake haskawa a tashar Youtube ta Aj Studio.

'Yar wasan barkwanci ta ce ba za ta auri wanda ya ta fi shi samun kuɗi ba
'Yar wasan barkwanci ta ce ta fi da yawa daga samarin da ke tunkararta samun kuɗi. Hoto: Ashmusy
Asali: Facebook

Ashmusy ta bayyana abinda ya hanata samun saurayi

Kara karanta wannan

To Fa: Miji Ya Tsorata, Ya Garzaya Kotu Yayin Da Matarsa Ta Yi Barazanar Sake Yi Masa Kaciya a Kano

Ashmusy ta bayyana cewa da yawa daga cikin samarin da ke tunkararta da nufin ƙulla alaƙa ta soyayya, ta fi su samun kuɗi a duk watan duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce a yanzu haka duk wanda ya tunkarota takan tambaye shi ko nawa ne yake samu a duk wata, saboda ta auna abinda yake samu da wanda take samu.

Ashmusy ta ƙara da cewa, ta fi son ta ga ta auri wanda ya fi ta kuɗi nesa ba kusa ba, amma ba wai wanda take ganin ta fi ba.

Ta kuma ce mafi yawan mazan da ta haɗu da su, ta fi su samun kuɗi a duk watan duniya.

Ba zan iya kwanciya da namiji domin kuɗi ba - Ashmusy

A wata hira da aka yi da 'yar wasan barkwanci a kwanakin baya wacce jaridar Vanguard ta wallafa, Ashmusy ta ce ba za ta iya kwanciya da namiji domin a ba ta kuɗi ba.

Kara karanta wannan

Me Ya Faru: NYSC Ta Tura Santaleliyar Budurwa Zuwa Mayanka Don Yi Wa Kasa Hidima, Bidiyon Ya Yadu

Ta ce aikace-aikace da sauran abubuwan da take yi suna kawo ma ta kuɗi fiye da abinda za a bai wa mace idan aka kwanta da ita.

Ta ce a yanzu haka tana da kasuwanci guda biyu da take tafiyar da su, wanda abinda suke kawo ma ta, ya fi ƙarfin ta je a kwanta da ita don a ba ta kuɗi.

Shan barasa ya kusa kai ni lahira - Pete Edochie

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan yadda shan barasa ya kusa aika fitaccen jarumin fim din Nollywood Pete Edochie lahira.

Jarumin ya bayyana cewa ya gamu da mummunan haɗarin mota da ya kusa zama sanadiyyar ajalinsa bayan ƙyanƙyamar barasa a shekarun baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel