Bacin Rana: Matar Aure Ta Fallawa Mai Wasan Barkwanci Mari Bayan Ya Nemi Su Sha Soyayya A Bidiyo

Bacin Rana: Matar Aure Ta Fallawa Mai Wasan Barkwanci Mari Bayan Ya Nemi Su Sha Soyayya A Bidiyo

  • Wani dan Najeriya mai wasan barkwanci, Deehans, ya sha mari bayan ya hadu da wata matar aure sannan ya nemi su kebe su sha soyayya
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, mai wasan barkwancin ya isa gaban matar sannan ya nemi ta bashi lambar wayanta, inda ta hana shi
  • Sai matashin ya bukaci matar auren da ta zo su kebe da juna, nan take ta wanke shi da mari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wata matar aure ta fusata bayan wani matashi ya isa gareta sannan ya nemi soyayyarta. A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, mutumin mai suna Deehans ya tunkari matar sannan ya nemi ta bashi lambar wayarta.

Cikin mutunci ta ki amsa bukatar shi sannan ta sanar da shi cewa tana da aure. Sai dai kuma, wannan amsa tata bai sa matashin ya halura ba inda ya nemi su kebe su sha soyayya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Alkalin Kotun Shari'a Zai Biya Wa Salele N100,000 Sadaki Don Auren Sahibarsa Bilkisu

Matar aure da matashi
Bacin Rana: Matar Aure Ta Fallawa Mai Wasan Barkwanci Mari Bayan Ya Nemi Su Sha Soyayya A Bidiyo Hoto: DeeHans
Asali: Instagram

Wannan ya tunzura kyakkyawar matar, inda ta wanka masa lafiyayyen mari. Bayan nan sai ta tsaya a bakin kofar sannan ta ja hankalin mijinta, nan take ya fito.

A wannan matakin ne, matashin ya yiwa ma’auratan bayanin cewa wasan barkwanci ne kawai, amma sai suka yi masa gargadi cewa kada ya kara kusantar inda suke.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Officialjoba ya ce:

“Bana yi kuma.”

Tariqq__x ya bayyana cewa:

“Mutum ta ce maka tana da aure, sannan kuma kana neman soyayyarta baa bun dariya bane.”

Emmy__moore ya ce:

“Ka sha ta kawai kenan. Yi hakuri dan uwa.”

Abdulrasheedjspark ya yi martani:

"Na’am ya yi maka kyau nagode Hajiya.”

Daga Wasa: Allkali Ya Aike Da Mai Wasan Barkwanci Gidan Maza Kan Firgita Banki Da Wasan Fashi Da Makami

Kara karanta wannan

Sabon Shiga: Bidiyon Yadda Matashi Ya Zunduma Ihu Cike Da Tsoro Bayan Ya Shiga Jirgin Sama A Karon Farko

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan shekaru 19 mai wasan barkwanci a Lagas, Eyinatayo Iluyomade, ya tsinci kansa a kurkuku bayan ya yi wasan barkwanci mai tsada ta hanyar ajiye wasikar fashi da makami a wani bankin zamani da ke garin Ondo, jihar Ondo.

Yan sanda sun gurfanar da Iluyomade a gaban kotu kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, barazana da kuma tin abubuwan da za su iya kawo barazana ga tsaro, jaridar Vanguard ta rahoto.

Dan sanda mai kara, Akao Moremi, ya fada ma kotu cewa wanda ake kara ya ajiye wata takarda a bankin yana nuna cewa da misalin karfe 1:00pm na wannan rana, mambobin kungiyarsa na fashi da makami za su zo yin fashi a bankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel