Dan wasan barkwanci Akpororo ya samu karuwa

Dan wasan barkwanci Akpororo ya samu karuwa

Fitaccen dan wasan barkwanci Jephthah Bowoto da aka fi sani da suna Akpororo ya samu karuwa bayan matarsa Josephine Ijeoma Onuabughuchi ta haifa masa diya mace.

A ranar litinin 30 ga watan agusta ne aka matar ta haihu, inda Akpororo ya daura hoton jaririyar a shafin sa na kafar sadarwa ta Instagram da taken “muna miki barka da shigowa masarautar RORO, muna godiya da farin cikin da kika kawo mana, nan gaba kadan zaki fara kirana da suna Baba, yake matar Bowoto, ina matukar kaunar ki”

Dan wasan barkwanci Akpororo ya samu karuwa

Idan ba’a manta ba, Akpororo ya fara haduwa da Josphine ne a shekarar 2014, daga bisani suka fara soyayya a 2015, ya nemi aurenta a ranar 2 ga watan agustan 2015. A ranar asabar 14 ga watan nuwamba ne aka daura auren Akpororo da matarsa a gidan shakatwa na Eagles dake unguwar surulere na jihar Legasa.

Muna yi ma Akpororo da matarsa murnar haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel