Hukumar NYSC Ta Tura Budurwa Zuwa Mayanka Don Yi Wa Kasa Hidima, Hotuna Sun Yadu

Hukumar NYSC Ta Tura Budurwa Zuwa Mayanka Don Yi Wa Kasa Hidima, Hotuna Sun Yadu

  • Wata budurwa mai bautar kasa ta tsinci kanta a mayanka don yi wa kasa hidima na shekara daya
  • Wata mai amfani da kafar Twitter ce ta wallafa budurwar inda ta ce ta santa sosai, wallafawar ta jawo martanin mutane da dama
  • Yayin da wasu ke kushe hukumar NYSC, wasu kuma cewa su ke yi hakan ya yi dai-dai watakila ta karanta harkar kula da dabbobi ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abin mamaki ya faru bayan tura wata santaleliyar budurwa mayanka don yin bautar kasa.

Budurwar ta shafe shekaru hudu ta na jami'a, gamawarta ke da wuya aka tura ta mayanka don yi wa kasa hidima.

Hukumar NYSC ta tura budurwa manyanka don bautar kasa
An Yada Bidiyon Budurwa Da NYSC Ta Tura Budurwa Mayanka. Hoto: Facebook/NYSC and Twitter/@TAAdeiye.
Asali: UGC

Wacece ta wallafa labarin budurwar?

TA Adeiye ita ta wallafa wannan labari a shafinta na Twitter wanda ya jawo martanin mutane da dama.

Kara karanta wannan

Dokar Hana Hijabi: Makarantu A Faransa Sun Dauki Mummunan Mataki Kan Dalibai Musulmai, Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Adeiye ta ce ta san 'yar bautar kasar na hakika wacce aka tura mayanka don yi wa kasa hidima.

Sai dai ba ta fadi inda abin ya faru ba ko kuma jiha ba inda ta ce hakan bai dace ba.

Ta tabbatar da hakan tare wallafa faifan bidiyo da kuma hotuna inda ta ce ta fara siyar da nama a shago.

A cikin faifan bidiyo an gano wani dauke da nama da kuma kafafun saniya a cikin bokiti.

Legit.ng ta tuntubi Adeiye don karin bayani amma har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba ta mai da martani ba.

Mutane da dama sun yi martani inda wasu ke cewa hakan ba matsala ba ce.

Yayin da wasu ke cewa watakila ta karanta harkar kula da dabbobi ne a jami'a amma ba a tabbatar da hakan ba.

Kara karanta wannan

“N330k Muka Siya”: Wani Mutum Ya Siya Motar Hannu, Kofar Ta Ki Budewa Bayan Ya Je Biki Da Ita

@theDamiDami:

"Kullum NYSC shirme su ke, sun tura abokina zuwa zuwa coci wanda ya karanta lissafin kudade."

@Olurantowoseeni:

"Zai iya zama abin dariya, amma hakan ya na da kyau, masu kasuwar za su karu daga mai ilimi idan su na son koya."

@niruha__:

"Watakila ta karanta harkar kula da dabbobi ne."

"Ku Daina Tura Matasan NYSC Zuwa Jihohin Kebbi Da Zamfara" Shinkafi

A wani labarin, Tsohon shugaban kwamitin hukunta 'yan bindiga a jihar Zamfara, Sani Shinkafi ya roki hukumar NYSC ta daina tura matasa zuwa jihohin da babu zaman lafiya.

Shinkafi ya bukaci NYSC ta dakatar da tura matasan masu hidima ga kasa zuwa jihohin da 'yan bindiga suka hana jama'a zaman lafiya a Arewacin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel