Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ranaku 2 A Matsayin Hutun Bikin Babban Sallah

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ranaku 2 A Matsayin Hutun Bikin Babban Sallah

  • Gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta sanar da ranakun hutun babbar sallah na shekarar bana
  • Tinubu ya ayyana ranakun Laraba, 28 ga watan Yuni, da Alhamis, 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun
  • Sanarwar ta fito ne ta hannun babban sakataren ma'aikatar harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da ranar Laraba, 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun babbar sallah wato Eid-El-Kabir.

Sanarwar dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade ya fitar ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Tinubu ya sanar da ranakun hutun babbar sallah
Shugaba Tinubu ya sanar da ranar Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutun babbar sallah. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya bayyana ranakun hutun babbar sallah

Sanarwar tana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Sabon Shugaban Yan Sanda Ya Shiga Ganawa da Manyan Kwamandoji, Bayanai Sun Fito

“Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Laraba 28 da Alhamis 29 ga watan Yunin 2023 a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan babbar sallah ta wannan shekarar, sannan tana yi wa al’ummar Musulmi na gida da na ƙasashen ketare barka da sallah.”
"Muna fatan addu'o'i da sadaukarwa da za a yi a wannan gagarumin biki, za su kawo mana zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya."

Sarkin Musulmi ya ayyana Laraba, 28 ga Yuni a matsayin ranar Sallah

A makon da ya gabata ne dai mai alfarma sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya sanar da ranar da za a gudanar da Idin babbar sallah ta bana.

Ya sanar da cewa za a gudanar da Idin ne a ranar Laraba, 28 ga watan Yunin 2023, wacce ta yi daidai da 10 ga watan Zhul-hijjah shekara ta 1444H.

Gwamnan Sokoto ya ba da umarnin biyan ma'aikata albashinsu kafin sallah

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Tarayya Ya Naɗa Mutane 33 a Manyan Muƙamai, Bayanai Sun Fito

A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ba da umarnin a biya ɗaukacin ma'aikatan jihar albashinsu kafin sallah babba.

Haka nan gwamna Aliyu ya ba da umarnin a biya 'yan fansho kuɗaɗensu domin suma su gudanar da bukukuwan Sallah lami lafiya.

Gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma'aikatan damar gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin walwala da kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel