Ga Su Suna Bi Na: Matashiya Ta Zauce, Ta Sha Alwashin Tona Abun da Ta Birne a Bidiyo

Ga Su Suna Bi Na: Matashiya Ta Zauce, Ta Sha Alwashin Tona Abun da Ta Birne a Bidiyo

  • Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wata matashiya yar Najeriya da ke neman tudun tsira da rayuwarta cewa wasu na bibiyarta
  • A bidiyon mai tsima zuciya, matashiyar ta fashe da kuka yayin da take rokon mutanen boyen da su daina bibiyar rayuwarta
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani sosai a kan bidiyon inda da dama suka shawarceta da ta tona sirrin da ke boye

Wata matashiya yar Najeriya ta haifar da martanoni masu tsuma zuciya daga jama'a bayan ta nuna hauka tuburan a titi.

A cikin wani bidiyon da ya yadu, an gano matashiyar cikin hawaye yayin da take gudun fanfalaki a titi, tana ihun 'zan tona asiri'.

Budurwa na hawaye
Ga Su Suna Bi Na: Matashiya Ta Zauce, Ta Sha Alwashin Tona Abun da Ta Birne a Bidiyo Hoto: @sugah515
Asali: TikTok

Ta yi ikirarin cewa mutane na bibiyar rayuwarta don kashe ta, sannan ta roki mutane da su kawo mata dauki, don bata so a kashe ta.

Kara karanta wannan

Zuciyar Zinare: Shehu Sani Ya Tsinci Jinjiri a Titi, Ya Mayar Da Shi Dansa

Da take ci gaba da bayani, matashiyar ta yi ikirarin cewa maharanta suna zaneta, kuma cewa radadin ya fara fin karfinta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce:

"Ga su nan suna bibiyata. Dan Allah zan tona asiri. Ku daina zane ni. Zan fada dan Allah."

Jama'a sun yi martani

@salome6739181659752 ta ce:

"Kawai ki tona asiri za ki tsira da sunan Yesu."

@sethbanks65 ta ce:

"Wayyo Allah dukkanmu muna bukatar taya matar nan da addu'a."

@faithhanne6 ta ce:

"Wannan shine karo na biyu da nake ganin wannan dan Allah me ke faruwa ne."

@rosejay300 ta yi martani:

"Dan Allah faaa menene sirrin boyen don ni ban fahimci komai ba a nan."

@garlandherring ta ce:

"Wasu na ba'a da wannan amma wasu yankuna na duniyar nan zahirin gaskiya ne, ku tayata da addu'a."

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Nake Biya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya a Lagas, Bidiyon Ya Ja Hankali

Za ku dandana kudarku: Uwa ta yi wa diyarta baki saboda ta yi aure babu saninta

A wani labarin, wata uwa ta yi wa diyarta ta cikinta baki saboda ta shiga daga ciki da sahibinta ba tare da saninta ba.

Fusatacciyar uwar ta yi wa diyar tata albashir da cewar za ta dandana kudarta a gidan miji tunda har ta yarda ta yi aure ba tare da amincewarta ko gayyatarta zuwa wajen taron ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel