Bidiyon Yar Najeriya Tana Tafiya Da Zakuna 2 Ba Tare da Tsoro Ba Ya Ba Da Mamaki

Bidiyon Yar Najeriya Tana Tafiya Da Zakuna 2 Ba Tare da Tsoro Ba Ya Ba Da Mamaki

  • Wata matashiya yar Najeriya ta dauki wani bidiyo da ke nuna jarumtarta yayin da take tafiya da zakuna biyu sai kace ba namun daji masu hatsari ba
  • Matashiyar ta bayyana abubuwa suka wakana tsakaninta da manyan namun dajin da kuma yadda masu kula da wajen shakatawar suka yi mata jagora
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa ba za su taba yin wannan kasadar ba don ana iya haduwa da bacin rana

Wata matashiya yar Najeriya mai suna @beverlyadaeze, ta wallafa wani bidiyonta tana jera tafiya tare da wasu zakuna biyu a wani wajen shakatawa a kasar Afrika ta Kudu.

Da take daukar bidiyo kan haka, matashiyar ta bayyana yadda ta cika da mamaki lokacin da suka bude wata kofa sannan zakunan suka fito suna tafiyarsu hankali kwance.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yaro Dalibin Najeriya Yana Shan Garin Kwaki Cikin Dalibai 'Yan Uwansa, Tamkar Yana Cin Shinkafa

Budurwa da zakuna
Bidiyon Yar Najeriya Tana Tafiya Da Zakuna 2 Ba Tare da Tsoro Ba Ya Ba Da Mamaki Hoto: @beverlyadaeze
Asali: TikTok

Jarumar mata da zakuna 2

Kafin ta jera da namun dajin, ta bayyana cewa masu kula da wajen shakatawar sun ba ita da kawayenta wasu sanduna a matsayin matakan kariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiyar ta bayyana cewa yayin da suke jera tafiya da namun dajin, ta yi kokarin kwantar da hankalinta lokacin da daya daga cikin zakunan ya juya kansa. Ta kuma dage cewa lallai a ba zakunan abinci kafin su hada tafiya da su.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Chisom Daveed ta ce:

"Ko kare ba zan iya hada tafiya da shi ba."

Mel ta tambaya:

"Ta yaya mutane ke iya dakewa don kada su ruga a huje?"

Jessica Mabasa ta ce::

"Na sani kawai idan da zan gwada wannan, nan take zakunan za su fara jin yunwa."

Lerato ta ce:

"Mutanen kauyena ba za su barni na ji dadin wannan ba."

Kara karanta wannan

Kin Tsufa Da Haihuwa: Matashiya Ta Fashe Da Kuka Wiwi Lokacin Da Ta Ji Mahaifiyarta Na Da Cikin ‘Da Na 5

NATORI ta ce:

"Cikin sauki zan tarwatse."

Lashesbylo_ ta ce:

"Ba da ni ba dan Allah bana yi."

Karamin yaro ya kwashi dadi bayan ya raka mahaifinsa siyan gasasshen nama

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan su ci karo da bidiyon ban dariya na wani karamin yaro da ya raka mahaifinsa wajen siyar da gasasshen nama.

Yayin da mai naman ke kunshe na mahaifinsa a leda, yaron ya mayar da nasa hankalin wajen gwagwiyar dakwalen kazar da ke kan teburin gabansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel