Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin hukunta Pinnick kan zargin sace biliyoyin kudin NFF

Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin hukunta Pinnick kan zargin sace biliyoyin kudin NFF

- Shugaban kasa Buhari ya bayar da umurnin gaggauta hukunta shugaban hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafa ta kasa (NFF), Amaju Pinncick

- Buhari ya bayar da wannan umurnin ne kan zargin da ake yiwa shugaban hukumar NFF na sama da fadi da biliyoyin kudaden hukumar

- Binciken EFCC ya nuna cewa NFF ta samu kudi akalla $16,417,761 daga hannun FIFA da CAF a cikin shekaru 2, wanda suka yi batan dabo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin gaggauta hukunta shugaban hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafa ta kasa (NFF), Amaju Pinncick, bisa zarginsa da rashawar biliyoyin kudade a cikin hukumar.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hannun kwamitin binciken fadar shugaban kasa, karkashin jagorancin Mr Okoi Obono-Obla, ta haramtawa Pinncik fita daga Nigeria zuwa wasu kasashen.

Wakilin jaridar Punch, a ranar Asabar, ya hada rahoton cewa Buhari ya bayar da umurnin hukunta Pinnick ne a lokacin da Obono-Obla ya gabatar da rahoton binciken badakalar da kwamitin ya gudanar akansa.

KARANTA WANNAN: Garabasa: Farashin rijistar kamfanonin kasuwanci ya koma N5,000 a hukumar CAC

Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin hukunta Pinnick kan zargin sace biliyoyin kudin NFF

Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin hukunta Pinnick kan zargin sace biliyoyin kudin NFF
Source: Twitter

Haka zalika, hukumar EFCC ta gudanar da wani bincike tare da hada rahoto kan shugaban NFF, inda ta mika rahoton ga shugaban kasar, tana mai sanar da shi irin badakalar rashawar da aka tafka a cikin NFF, da kuma wadanda ke da hannu a ciki.

Buhari wanda rahotanni suka bayyana cewa ya harzuka ganin wannnan rahoton, ya bayar da umurnin hukunta Pinnick cikin gaggawa. Ya umurci Magu da ya gaggauta fara bincike kan yadda aka tafiyar da kudaden hukumar ta NFF.

A cewar EFCC, tuni ta fara gudanar da cikakken bincike kan kudaden da suke shiga da fita a asusun NFF, inda ta gano cewa hukumar NFF ta samu kudi akalla $16,417,761 daga hannun FIFA da CAF, daga watan Janairu 2014 zuwa watan Yuni, 2016. Kudin sun shiga ne ta bankunan Zenith da UBA, kamar haka:

 • 18/12/2014 Zenith Bank, Ac No: 5070407456, $8,400,000 (FIFA);
 • 23/01/2015, Zenith Bank, Ac No: 5070407456, $450,000 (FIFA);
 • 25/03/2015, Zenith Bank, Ac No: 5070407456, $1,081,000 (CAF);
 • 13/10/2015 Zenith Bank, Ac No: 5070407456, $3000 (CAF);
 • 12/01/2014, UBA, Ac No: 3000004944, $1,500,000 (FIFA);
 • 15/01/2014 UBA, Ac No: 3000004944, $1,746,745 (CAF);
 • 19/03/2014 UBA, Ac No: 3000004944, $249,950 (CAF);
 • 12/12/2014 UBA, Ac No: 3000004944, $301,467 (FIFA);
 • 14/05/2015 UBA, Ac No: 3000004944, $30,000 (FIFA);
 • 31/07/2015 UBA, Ac No: 3000004944, $315,149 (FIFA);
 • 14/08/2015, UBA, Ac No: 3000004944, $399,000 (FIFA);
 • 11/09/2015 UBA, Ac No: 3000004944, $300,000 (FIFA);
 • 16/10/2015, UBA, Ac No: 3000004944, $850,149 (FIFA);
 • 18/11/2015, UBA, Ac No: 3000004944, $2,990 (CAF);
 • 12/02/2016, UBA, Ac No: 3000004944, $79,540 (FIFA);
 • 15/03/2016, UBA, Ac No: 3000004944, $299,000, (CAF);
 • 22/06/2016 UBA, Ac No: 3000004944, $9,930 (CAF).

Magu a cikin rahoton, ya sanar da Buhari cewa tuni EFCC ta gudanar da bincike kan makamancin wannan laifi inda ta gurfanar da Chrstopher Andekin; Shugaban sashen kudi da mulki na NFF, Jafaru Mamzah da kuma kashiyan hukumar, Rajan Zaka, gaban mai shari P.O. Affem na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja,a ranar 15 ga watan Oktoba, 2018, akan aikata laifuka 5 da suka hada da hadin baki da kuma cin amanar aikin gwamnati da rashawa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel