Shugaban FIFA Infantino, ya bayyana kudirin sa na World Cup

Shugaban FIFA Infantino, ya bayyana kudirin sa na World Cup

 

– Gianni Infantino ya kawo kudirin kara Kasashen da ke zuwa Gasar Kofin Duniya ‘World Cup’ zuwa kasashe 40 daga Shekarar 2026.

– Nahiyar Afrika za ta samu Karin gidaje biyu a Gasar World Cup, idan har Kungiyar FIFA ta amince da wannan tsari.

– Kasashe 32 za su fafafta a Gasar da za ayi a Kasar Russia a 2018 da kuma Qatar 2022.

Shugaban FIFA Infantino, ya bayyana kudirin sa na World Cup

 

 

 

 

 

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Duniya (Watau FIFA), Gianni Infantino ya bayyana cewa Nahiyar Afrika za ta samu Karin gidajen duro har biyu, muddin aka amince da kudirin sa na kara yawan kasashen da za su je Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya (Watau World Cup). Shugaban na FIFA, Gianni Infantino yana so a kara yawan kasashen da ke buga Gasar ta World Cup zuwa 40 a shekarar 2026. Shugaba Infantino na FIFA yace idan har aka kara yawan kasashen daga 32 zuwa 40, to Afrika za ta samu Karin gidaje biyu. Infantino Gianni ya kawo wannan kudirin ne tun kafin a zabe shi a matsayin Shugaban Kungiyar Kwallon Kafar ta Duniya (FIFA) a watan Febrairu. A wannan tsari da ake kai, Afrika na da tukunya 5 ne kacal, idan har aka amince da kudirin Infantino na kara kasashen zuwa 40 daga 32, Afrika za ta samu tukunya 7 kenan a Gasar World Cup na duniya.

KU KARANTA: SHUGABAN FIFA YA ZIYARCI SHUGABAN KASAR NAJERIYA

Infantino Gianni yace: “Ni kudiri na shine a kai Kasashe 40, idan kuma aka amince da hakan , to akalla, Afrika ta samu Karin tukwane biyu.” Sai dai wannan tsari zai iya aiki ne kawai daga Gasar shekarar 2026, domin kuwa yanzu an kammala shirin Gasar 2018 da za a gabatar da Kasar Russia da kuma wanda za ayi a Qatar a shekarar 2022, dukkanin su dai, kasashe 32 ne za su kara. Yanzu haka dai, shi kan sa Shugaban FIFA din, ana binciken sa da saba wasu dokokin Kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng