Ina son in gaji Buhari a 2023, In ji Fasto Tunde Bakare

Ina son in gaji Buhari a 2023, In ji Fasto Tunde Bakare

- Shugaban cocin Citadel Global Church, Fasto Tunde Bakare ya ce yana son zama shugaban kasar Najeriya

- Bakare ya yi takara tare da Shugaba Muhammadu Buhari a karkashin jam'iyyar CPC a 2011 amma babu nasara

- Bakare ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Legas

Shugaban cocin Citadel Global Church, Pastor Tunde Bakare, ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban kasar Najeriya.

Ya ce idan ya dama, ya so ya gaji shugaba Muhammadu Buhari.

Bakare wanda yayi takara da Buhari lokacin da ya tsaya a jam'iyyar CPC da aka rushe, ya tattauna da manema labarai a Legas.

Ina son in gaji Buhari a 2023 - Tunde Bakare
Ina son in gaji Buhari a 2023 - Tunde Bakare. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Malamin cocin, wanda ya cika shekara 66 yau (11 ga Nuwamba), ya ce zai samar da sabuwar Najeriya yadda kishin kai zai zama hanyar samar da ci gaban kasa.

DUBA WANNAN: Wani dan majalisa ya fice daga majalisa yayin da minista ke kare kasafin kudi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Bakare ya sha bayyana aniyarsa ta shugabancin kasar nan sai dai bai bayyana jam'iyyar da zai tsaya takara ba. Yanzu dai ba dan kowace jam'iyya bane.

Da aka tambaye shi ko har yanzu yana sha'awar takarar, sai ya ce, "akwai wani abu da ake cewa kaddara. Ni bazan boye komai ba, burina bazai zama kamar manufa ba, bana hadawa.

KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

"Ba magana ce ta rayuwa da mutuwa ba, amma zaka iya rubutawa, indai ubangiji yana raye, kuma ya bani damar, ranar zai zama kamar yadda Joe Biden ya zama, nima zan zama shugaban Najeriya."

Da yake ci gaba da jawabi, Bakare ya goyi bayan a daidaita tsarin amfani da kafafen yada labarai saboda hadarin yada labaran karya.

A wani labarin, an samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk gabatar ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164