Tirkashi: An kai karar jaririya 'yar wata 6 kotu

Tirkashi: An kai karar jaririya 'yar wata 6 kotu

- Wata kotu da ke Brussel ta yi wa wata jaririya mai watanni shida a duniya sammaci

- Kotun ta zargi jaririyar mai watanni shida ne da laifin karbar kudin haya ba yadda yake da pam 500

- Mahaifiyar jaririyar ta ce a lokacin da abin ya faru, ba a haifa diyar ba saboda haka akwai yuwuwar kuskure ne

An zargi wata jaririya mai watanni shida kacal a duniya da karban kudin hayan da ya wuce na misali da pam 500. An maka jaririyar ne a wata kotun Brussels.

Jaririyar wacce babban alkalin Brussels municipality of Molenbeek-Saint-Jean ya bukaci ta garzayo kotun, ana zarginta ne da karbar kudin hayan da ya zarta da pam 500 a kan wata kadara da aka bada haya ta hannun Public Centre for Social Action (CPAS).

Wannan lamarin ya faru ne daga watan janairu zuwa watan Yuni na 2019, kafin haihuwar jaririyar a watan Yuli.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, mahaifiyar yarinyar ta wallafa labarin wasikar da ta same ta na sammacin diyarta mai watanni 6 kacal a duniya. Ta ce akwai yuwuwar kotun tayi kuskure ne.

KU KARANTA: Kwalba ta buga mini a kai ni kuma na kasheta - Cewar saurayin da ya kashe budurwarshi a Bauchi

Kamar yadda mahaifiyar ta ce, “Wani magatakarda ya tabbatar min da cewa kuskure ne aka yi. Amma kuma sai na samu wasika kashi ta biyu daga kotun inda aka bukaceni da in je tare da nuna wa alkali jaririyar don tabbaci.”

“A lokacin da na kira kotun, na sanar da su cewa bani da kudin motar zuwa Brussel kuma a lokacin da abin ya faru ko haihuwar yarinyar ba a yi ba.”

Daga baya mahaifiyar ta ce ta samu sako ta yanar gizo inda aka ce alkalin da lauyan sun hakura da karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel