Jihohin da Suka Fi Samun Kudi daga Kason Tiriliyoyin FAAC a Shekarar 2025

Jihohin da Suka Fi Samun Kudi daga Kason Tiriliyoyin FAAC a Shekarar 2025

  • A rabon kudin da aka yi a kwamitin FAAC a shekarar da ta wuce, jihohi 12 kadai sun samu N4.21tr
  • Jihohin kudu maso kudu da suke da arzikin mai sun tashi da 51% na abin da aka raba masu
  • Kano da Katsina sun shiga sahun farko albarkacin yawan kananan hukumomin da ke jihohin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Alkaluman da aka fitar sun nuna irin makudan kudin da wasu jihohi suka samu daga kason FAAC.

A kowane wata ana raba abin da ya shigo cikin asusun tarayya tsakanin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

Gwamnoni
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Gwamnonin jihohi a Aso Rock Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

Yadda ake yi wa jihohi kaso a FAAC

Statisense a X ta tattaro duka kudin da suka shiga hannun jihohin da aka fi yin rabon da su a shekarar da ta wuce.

Ana hada abin da ya shigo asusun Najeriya daga saida mai, sauran ma'adani da ta karbar haraji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa mace mai ciki da jariri ta'addanci a Kaduna

Daga nan aka fahimci cewa jihohin da suke da arzikin mai su ne a gaba idan ana zancen kason da aka yi a tarayya.

Bayan an ba kowace jiha kudinta daidai da yawan kananan hukumomi da mutane, ana duba masu arzikin mai.

Akwai karin 13% da doka ta tanada ga Delta, Rivers, Akwa Ibom da Bayelsa wadanda suke da rijiyoyin danyen mai.

FAAC: N4tr ya shiga aljihun jihohi 12

Jihohi 12 da ke sahun gaba sun tashi da fiye da N4.2tr daga watan Junairu zuwa Disamba a shekarar ta 2025.

64% na kudin da ake magana a kai wato kusan N2.7tr sun shiga alijuhunan jihohi biyar na farko duk daga bangaren Kudu.

Kudin da shiyyoyi suka samu a 2025

Yankin Kudu maso kudu ya tashi da fiye da rabin kudin saboda kason da ake ba jihohin da suke a shiyyar Neja-Delta.

Legas, Oyo da Ondo su ne jihohin kudu maso yamma da suka shiga wannan sahu, sun samu kusan 20% na kudin.

A Arewa maso yamma kuwa, Kano da Katsina ne kawai a ciki domin su biyu sun raba N482bn a cikin watanni 12.

Kara karanta wannan

Iyalan sojoji da dukkan dakarun da ke cikin jirgin sojin da ya yi hadari sun mutu

Borno ce kadai ta samu shiga daga Arewa maso gabas. Jihar mai kananan hukumomi 27 ta samu N204bn a 2025.

Kamar dai Arewa ta gabas, a Kudu maso gabas ma Anambra ce kadai ta samu kudi sosai daga FAAC, ta samu N204bn.

Ita ma Abuja wanda ita ce birnin tarayya ta samu N204bn, kusan 5% na kason jihohin nan 12.

Jihohin da suka fi samun kudin FAAC

1. Delta — ₦657.7bn

2. Lagos — ₦531.5bn

3. Rivers — ₦516.9bn

4. Akwa Ibom — ₦498.0bn

5. Bayelsa — ₦488.2bn

6. Kano — ₦279.7bn

7. Oyo — ₦221.2bn

8. Borno — ₦204.8bn

9. Anambra — ₦204.6bn

10. FCT — ₦204.4bn

11. Ondo — ₦204.1bn 12

12. Katsina — ₦203.2bn

Jihohin da suka fi kokari a NECO

Kuna da labari cewa bayanan sakamakon NECO na 2026 sun kunyata daliban da ake da su a jihohi 19 na yankin Arewacin Najeriya.

Yaran da suka yi jarrabawa a Abia da Ebonyi daga Kudu maso gabas suna cikin wadanda suka fi samun nasara a shekarar nan

Yayin da Kudu suka mamaye jihohi 10 na farko, babu ko daya daga Arewa duk da Kano ta fi kowa zunzurtun wadanda suka ci jarrabawar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng