Dalilin da yasa na koma APC - Bala Tinka

Dalilin da yasa na koma APC - Bala Tinka

- Shugaban kamfen din PDP na jihar Gombe, Bala Bello Tinka ya ce ya fice daga PDP ne saboda taimakawa Shugaba Buhari lashe zabe karo na biyu

- Bala Bello Tinka ya kara da cewa jituwar da ke tsakanin shugabanin PDP da suka gaza warwarewa yana daga cikin dalilan da yasa ya fice daga jam'iyyar

- Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari da sauran shugabanin APC za su yiwa Bala Tinka maraba da shigowa APC a yau Asabar wurin kamfen a Gombe

Dalilin da yasa na koma APC - Shugaban kamfen na PDP

Dalilin da yasa na koma APC - Shugaban kamfen na PDP
Source: Facebook

Shugaban yakin neman zaben jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe, Alhaji Bala Bello Tinka ya ce ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne domin ya taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari zarcewa karo na biyu.

A wata hirar wayar tarho da yayi da Daily Trust, Bala Tinka ya ce ya fice daga PDP ne saboda rashin jituwar da ke tsakanin jiga-jigan jam'iyyar PDP wadda aka kasa warwarewa kuma domin ya bude sabon shafi a siyarsa.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun halaka direba a hanyar Birnin Gwari

Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari da sauran shugabanin jam'iyyar za su yiwa Bala Tinka wankan tsarki na shiga APC a wurin kamfen din da za a gudanar a garin Gombe a yau Asabar.

An nada shi Direkta Janar na kamfen din jam'iyyar PDP ne a Disambar bara.

A 2015, ya yi amfani da shirinsa na Talba Neighbour to Neighbour domin taka muhimmiyar rawa wurin ganin Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya lashe zabe karo na biyu.

Ana ganin rawar da Tinka ya taka ta taimaka wurin kare Dankwambo daga guguwar jam'iyyar APC da tayi awon gaba da jihohin Arewa 16 a zaben 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel