Za a haramtawa wasu Wayoyin salula whatsapp

Za a haramtawa wasu Wayoyin salula whatsapp

Miliyoyin wayoyi za su daina amfani da whatsapp

- Daga karshen shekarar nan, za a haramtawa wasu salula whatsapp

- Wayoyi na kirar Android, Windows da IOS za su gamu da matsala

Za a haramtawa wasu Wayoyin salula whatsapp

 

 

 

 

 

Wayoyin salula da dama irin na zamani za su gamu da cikas zuwa karshen wannan watan na Disamba. Za a haramtawa wayoyi da dama amfani da kafar sadarwa ta whatsapp kawo karshen wannan shekarar.

Gidan Facebook ne dai suka saye kamfanin whatsapp a kwanakin baya, miliyoyin mutane dai kuwa suna amfani da kafar whatsapp wajen aika sakonni. Sai dai masu wayoyi irin na da; kamar su Windows, Android da IOS ba za su samu damar cigaba da amfani da whatsapp ba.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kai hari

Whatsapp din tace tsofaffin wayoyin ba za su iya cigaba da amfani da manhajar ba, watakila har sai nan da zuwa shekarar mai zuwa. Wayoyi irin su Apple da tsofaffin Android za su bar whatsapp.

Haka nan ma kuwa masu wayar Blackberry da Nokia za su gamu da babban cikas na amfani da manhajar whatsapp har sai nan da tsakiyar shekara mai zuwa. An dai dade ana amfani da whatsapp wajen aika sakonni.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

Asali: Legit.ng

Online view pixel