Kimiyya: Najeriya ta samar wa duniya sabbin kaji da suka zarta na saura a maiqo

Kimiyya: Najeriya ta samar wa duniya sabbin kaji da suka zarta na saura a maiqo

- Jami'ar tarayya ta noma da kiwo dake Abeokuta ta bar tarihi

- Kafa tarihin ya dau aikin shekaru 24 ne

- Hakan kuma zai kawo cigaba ga mutane da Kasar Najeriya

Kimiyya: Najeriya ta samar wa duniya sabbin kaji da suka zarta na saura a maiqo
Kimiyya: Najeriya ta samar wa duniya sabbin kaji da suka zarta na saura a maiqo
Asali: UGC

Jami'ar tarayya ta noma da kiwo dake Abeokuta (FUNAAB) ta kafa tarihin kaza mai aure bayan shekaru 24 ana bincike.

Shugaban jami'ar, Farfesa Kolawole Salako yace wannan nasarar ta dau shekaru 24 na aiki tukuru da jajircewa. Yace wannan zai kawo cigaba ga mutane da kuma kasar a kasuwar kaji da kuma samar da abinci a Najeriya.

Kazar da suka saka mata suna 'FUNAAB Alpha' yace ta samu karbuwa ga mutanen karkara da masu kiwo. An yi wa aikin rijista da suna FUNAAB Alpha a ranar 26 ga watan yuli, 2018.

Zakaran gidan da zata iya kai nauyin 2.1 zuwa 2.6kg a cikin sati 20, sai Kazar na kai 1.6 zuwa 1.8kg, sai kawai 200 zuwa 250 a shekara, inji shugaban jami'ar.

DUBA WANNAN: Tattaunawa da Mulhidan Najeriya

Ya jinjiinawa kungiyar masu binciken da farfesa Olifunmilayo Adebambo ya jagoranta, saboda aikin da sukayi na tsawo shekaru 24 ba tare da gajiyawa ba. Shugaban ya jinjiinawa kungiyar Bill and Melinda Gates Foundation, masu ruwa da tsakin da suka dau nauyin binciken da ya samar da "cibiyar binciken Tauraruwa FUNAAB" a jami'ar.

Yayi kira ga Gwamnatin tarayya da kuma masu ruwa da tsaki dasu tallafi shirin domin samar da abinci mai dorewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel