Kudin ruwa ya na tagayyara ma su kiwon kaji

Kudin ruwa ya na tagayyara ma su kiwon kaji

Ma su kiwon kaji na gidan gona sun koka da koma bayan da su ke fuskanta sanadiyar tashin kudin ruwa da bankunan kasar nan su ke karba a wajen biyan bashi

Shugaban ma su kiwon kaji na gidan gona na Najeriya (Poultry Association of Nigeria, PAN), Dr. Ayoola Oduntan ya bayyan korafin cewa kudin ruwa da bankunan kasar nan su ke karba ya janyo koma baya wajen kasuwancinsu.

Oduntan ya bayyana hakan ne a wani taron masu kiwon kajin gidan gona na duniya da a ka gabatar a jihar Legas

A rahoton na shi ya bayyana cewa bankunan kasar nan su na bukatar duk wanda ya zai karbi bashi to sai ya biya kaso 27 na kudin wajen biyan bashin.

Kudin ruwa ya na tagayyara ma su kiwon kaji
Kudin ruwa ya na tagayyara ma su kiwon kaji

Yace wannan kashi 27 na kudin ruwa da bankunan ke karba daga hannun ma su kiwon kaji kadai ya isa ya hana wasu shiga harkar kuma ya dakusar da wanda su ke cikin harkar ta kiwon kaji.

Shugaban ya kara kokawa da ire-iren kalubalen da su ke fuskanta wajen samar da kayan aiki da kuma tsadar kayan abincina kaji sanadiyar tashin dalar Amirka a kasar nan.

KU KARANTA: Ma'aikatan tsaron kan hanya sun yi sanadiyar wani hatsari a jihar Enugu

Ya kara da cewa banda wannan kadai akwai mastalolin rashin kasuwa da suke fuskanta a kasar nan da kuma shigo da kayan aikin na gonar kaji ta barauniyar hanya da ya ki ci-ya ki cinyewa.

A karshen shugaban kungiyar ta masu kiwon kaji ya ke kira ga gwamnatin kasar da ta yi duba zuwa tashin da farashin kudin ruwa ya yi a kasar nan.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng