Kwandasta ya sace wa fasinja katin ATM, ya cire N82,000

Kwandasta ya sace wa fasinja katin ATM, ya cire N82,000

Wani kwandastan mota mai shekaru 34 ya shiga hannun 'yan sanda a kan zarginsa da sace katin ATM din fasinja. Dolapo Pine a ranar Litinin ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Tinubu a jihar Legas, sakamakon kwashe N82,000 da yayi daga asusun bankin fasinja.

'Yan sandan sun gurfanar da Pine mazaunin Jakande ne da ke Isolo a jihar Legas da laifuka biyu. Amma sai ya musanta zargin da ake masa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Ajaga Agboko, ya sanar da kotun cewa wanda ke kare kansa din ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Fabrairun 2020, wajen karfe 8 na safe a tashar motar Chisco da ke Lekki.

Ya ce wanda ake zargin ne kwandastan motar mai karar. Sun hada baki da direban motar da ta hau ne inda suka sace mata katin ATM da waya kirar Tecno wacce za ta kai N6,000, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwandasta ya sace wa fasinja katin ATM, ya cire N82,000
Kwandasta ya sace wa fasinja katin ATM, ya cire N82,000
Asali: UGC

DUBA WANNAN: A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa

"Wanda ake zargin tare da direban sun tirsasata inda ta sanar da su lambobin katin kafin daga bisani su hankadota daga motar. Sun kuwa yashe mata N82,000 daga asusun bankin nata. Daga bisani an kama wanda ake zargin amma har yanzu ba a kama direban ba," mai gabatarwar ya ce.

Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashi na 287 da 411 na dokokin laifukan jihar Legas na 2015.

Majistare T. A. Anjorin-Anjose ta bada belin wanda ake zargin a kan N200,000 tare da tsayayyu guda biyu.

Anjorin-Anjose ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 3 ga watan Maris 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel