Tinubu Ya Duba Arewa, Ya Zabo Mutumin da Yake So Ya Zama Mataimakin Gwamnan CBN
- Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon shugaban SEC Lamido Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)
- An rahoto cewa Lamido Yuguda kwararre ne wanda ya taba yin aiki a asusun lamuni na duniya IMF da kuma babban bankin kasa na tsawon shekaru
- Wannan nadi yana jiran amincewar majalisar dattawa yayin da tsohon mataimakin gwamnan Bala Bello ya zama mai ba shugaban kasa shawara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki wani muhimmin mataki na sake fasalin shugabancin babban bankin Najeriya ta hanyar naɗa sabon mataimakin gwamnan CBN.
Tinubu ya nada tsohon shugaban hukumar kasuwancin hannun jari (SEC), Malam Lamido Abubakar Yuguda, a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin kasar.

Source: Twitter
Tinubu ya nada sabon mataimakin gwamnan CBN
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a yammacin ranar 11 ga Maris, 2026.
Wannan naɗi, wanda ke jiran amincewar majalisar dattawa kamar yadda sashi na 8(1) na dokar babban bankin ƙasa ta shekarar 2007 ya tanada, ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke buƙatar ƙwararrun masana domin tunkarar ƙalubalen tattalin arziki.
A cewar sanarwar Onanuga, Shugaba Tinubu ya zaɓi Yuguda ne sakamakon gogewarsa ta shekaru da dama a harkar banki da kasuwancin duniya.
"Wannan naɗi ya biyo bayan sauya wa tsohon mataimakin gwamnan bankin, Bala Bello, wurin aiki, inda aka naɗa shi a matsayin bai ma shugaban kasa shawara na musamman kan tattalin arzikin siyasa."
- Bayo Onanuga.
Tarihin gogewar Yuguda a fannin kuɗi
Lamido Yuguda ba baƙo ba ne a harkar tafiyar da manufofin kuɗi na Najeriya da ma duniya baki ɗaya ba. Ya fara aikinsa a bankin CBN tun a shekarar 1984 a matsayin babban mai kula da sashen ayyukan ƙasashen waje.
"Kwararre ne wanda ya kammala digirinsa a fannin Akanta daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1983, kuma mamba ne a ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta ƙasa (ICAN).
"Ya kwashe fiye da shekaru 30 yana aiki a cikin tsarin tafiyar da kuɗi na Najeriya, inda ya kai matsayin daraktan kula da asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasar kafin ya yi ritaya a 2016."

Kara karanta wannan
Ganin fetur ya tashi a duniya, Tinubu ya bada umarnin gaggawa a kawo wa 'yan Najeriya sa'ida
- Bayo Onanuga.
Baya ga aikin sa a cikin gida, sanarwar ta ce Yuguda ya yi fice a duniya, inda ya yi aiki a matsayin masanin tattalin arziki a Asusun Lamuni na Duniya (IMF) tsakanin 1997 zuwa 2001.

Source: Twitter
Abubuwan da ke gaban Yuguda a CBN
A can, ya bayar da gudunmawa wajen tsara manufofin tattalin arziki ga ƙasashe da dama na nahiyar Afirka. Daga shekarar 2020 zuwa 2024, ya kasance shugaban hukumar SEC, inda ya jagoranci gyare-gyare masu ma'ana da suka dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a kasuwar hannun jari ta Najeriya.
Shugaba Tinubu ya buƙaci Yuguda da ya yi amfani da dukkan ƙwarewarsa wajen tabbatar da dorewar darajar Naira da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, in ji rahoton The Cable.
Ana sa ran cewa idan Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi, haɗin gwiwar sa da Gwamnan CBN na yanzu zai haifar da sababbin dabarun magance hauhawar farashin kaya da kuma ƙarfafa tsarin bankunan ƙasa.
Karanta sanarwar Onanuga a nan kasa:
An yi barazanar kama gwamnan CBN
A wani labari, mun ruwaito cewa, majalisar Wakilai ta yi barazanar bayar da sammacin kama gwamnan CBN, Olayemi Cardoso bisa zargin raini da rashin mutunta ta.
Kwamitocin Majalisa kan binciken kasafin kudi da kadarorin gwamnati ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar bayan wani zama da suka gudanar.
Sun ce gwamnan CBN ya take umarnin da aka basa kan kuɗin asusun da aka daina amfani da su kuma ya ki amsa gayyatar da aka tura masa.
Asali: Legit.ng

