Buhari ya yi naɗe-naɗen muƙamai 141 cikin kwanaki 81 - Bincike

Buhari ya yi naɗe-naɗen muƙamai 141 cikin kwanaki 81 - Bincike

Wani bincike da manema labarai na jaridar Daily Trust suka gudanar, ya nuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai 141 cikin kwanaki 81.

Binciken ya nuna cewa, wannan shi ne mafi girma ta fuskar yawan naɗe-naɗen muƙamai da Buhari yayi tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Jerin gwanon naɗe-naɗen muƙaman a Ma'aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati, ya fara kunno kai ne tun a farkon watan Afrilu, yayin da gwamnatin tarayya ta shimfa dokar kulle saboda annobar korona.

Wannan yunkuri na naɗe-naɗen muƙamai da shugaban kasar ya yi ya ba wa maraɗa kunya masu tuhumarsa da cewa yana tafiyar hawainiya wajen gudanar aikace-aikace.

Lamarin da ya sanya wasu 'yan kasar suka kakaba masa suna da "Baba-Go-Slow".

Ana iya tuna cewa a watan Yunin 2019 ne shugaba Buhari ya sha alwashin baiwa wadanda suke kiransa da sunan "Baba-Go-Slow" mamaki yayin wa’adin mulkinsa na biyu.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta kafar talabijin din Najeriya ta kasa wato NTA.

Buhari ya yi naɗe-naɗen muƙamai 141 cikin kwanaki 81 - Bincike
Buhari ya yi naɗe-naɗen muƙamai 141 cikin kwanaki 81 - Bincike
Asali: Facebook

Ga jerin naɗe-naɗen muƙamai da shugaban kasar ya yi tare da kwanan watan da aka yi su:

Bassey Edet - Shugaban Asibitin Mahaukata na Calabar - Ranar 2 ga watan Afrilu.

Aisha Adamu - Shugaban Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, Jalingo - Ranar 2 ga watan Afrilu.

Musa Ahmed - Shugaban Jami'ar Noma ta Zuru a jihar Kebbi - Ranar 9 ga watan Afrilu.

Naɗin Muheeda Dankaka da mambobi 38 na Hukumar Kula da Da'ar Ma'aikata - Ranar 28 ga watan Afrilu.

AVM Muhammadu Alhaji Muhammed (Rtd) - Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) - Ranar 2 ga watan Mayu

Sunday Thomas - Babban Kwamishina kuma Shugaban Hukumar Inshora (NAICOM)

A watan Yuni ne majalisar dattawa ta amince da nadin Mrs. Diana Okonta da Mrs. Ya’ana Talib Yaro a matsayin Daraktoci biyu na Hukumar kare hakkin masu ajiya a bankuna NDIC.

Prof. Jummai A.M. Audi, Bassey Dan-Abia da Mohammed Ibraheem - Daraktoci uku na Hukumar Kula da Shari'a NLRC - Watan Afrilu.

KARANTA KUMA: APC ta fara gudanar da zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo

A ranar 15 ga watan Yuni, fadar shugaban kasa ta ba sanarwar sauye-sauye a hukumar NBET da ke karkashin ma’aikatar wutar lantarki.

Buhari ya tabbatar da Dr. Nnaemeka Ewelukwa a matsayin shugabar NBET.

Sauran darektocin da aka nada sun hada da Alex Okoh, Patience Oniha, Injiniya Musatafa Balarabe Shehu, Suleymen Ndanusa, da Adeyeye O. Adepegba.

Alwan Hassan - Mukaddashin Darakta Janar na Bankin Manoma (BOA) - Ranar 5 ga watan Mayu

A ranar 6 ga watan Mayu, Buhari ya nada IGP Suleiman Abba, a matsayin shugaban majalisar amintattu da Asusun Kula da Hukumar 'Yan sanda (NPTF).

Sai kuma Ahmed Aliyu Sokoto a matsayin sakataren NPTF.

A ranar 12 ga watan Mayu, majalisar dattawa ta amince da nadin jakadu 42 da shugaban kasar ya aike mata da sunayensu.

KARANTA KUMA: Kakakin Majalisar Gombe ya warke daga cutar Korona

Haka zalika a wannan rana, Buhari ya amince da nadin Paul Ikonne, a matsayin babban sakataren Hukumar Habaka Filayen Noma na Kasa, NALDA.

A ranar 13 ga watan Mayu, Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

A nada Kashim Ibrahim-Imam a matsayin shugaban hukumar TETFUND a ranar 19 ga watan Mayu.

A ranar 19 ga watan Mayu, an nada Lamido Yuguda a matsayin babban daraktan hukumar zuba hannun jari ta Najeriya, watau Securities and Exchange Commission.

Shugaba Buhari ya kuma nemi majalisar ta amince da nadin mutum 7 a matsayin Darektocin Hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya (RMAFC).

KARANTA KUMA: Hukumar JAMB ta bayyana sunayen dalibai 13 da suka fi yin fice a jarabawar bana

Sun hadar da Salamatu Mohammed Bala (Adamawa), Alfred Egba (Bayelsa), Adamu Shettima Yuguda (Borno), Oladele Semiu Gboyega (Osun), Bello Abubakar Wamakko (Sokoto), Ahmed Yusuf (Taraba), Barr. Emmanuel Nwosu (Imo).

Nadin Mr. Sule Abdulaziz a matsayin sabon shugaban kamfanin rarraba wutar lantarki.

A ranar 22 ga watan Mayu, Buhari ya nada Farfesa Godswill Obioma a matsayin sabon shugaban Hukumar NECO.

A ranar 20 ga watan Mayu, aka nada sabbin Darektocin Kula da Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC).

Sun hadar da; Mohammed Lawal, Tajudeen Umar, Adamu Mahmood Attah, Sanata Magnus Abe , Dr. Stephen Dike da Cif Pius Akinyelure.

Sai kuma Darakta Janar na Hukumar Sadarwa NCC, Farfesa Umar Dambatta, da majalisar ta amince bayan shugaba Buhari ya sake sabunta nadin mukaminsa a wa'adi na biyu.

A baya bayan nan ne cikin watan Yuni, majalisar dattawa ta amince da mai shari'a Monica Dongbam-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

A ranar 16 ga watan Yuni, Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ta ba da sanarwar nadin sabbin sakatarorin dindindin 12 a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel