DSS na Shirin Gayyatar Yaran El Rufa'i, Matar Dadiyata Ta Yi Magana kan Dauke Mijinta
- Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sake bude binciken batan Abubakar Idris da aka fi sani da Dadiyata bayan shekaru bakwai
- Binciken na zuwa bayan ikirarin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi game da sace matashin da ya yi shahara a sukar gwamnati
- Matarsa, Khadija ta roki ‘yan Najeriya su taimaka gano halin da yake ciki, a sanar da su domin hankalinsu ya kwanta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na u. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Hukumar tsaro ta farin kaya, (DSS), ta sake bude bincike kan batan Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tana shirin gayyatar wasu da ake zargi domin amsa tambayoyi kan lamarin.

Source: UGC
Jaridar Punch ta wallafa cewa Dadiyata, malami a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina, ya bace ne tun ranar 1 ga Agustan 2019.
Wasu ‘yan bindiga sun dauke shi daga gidansa da ke Barnawa a Kaduna. Har yanzu, kusan shekaru bakwai kenan ba a san inda yake ba.
Rokon matar Dadiyata kan bacewar mijinta
Khadijah, matar Dadiyata, ta sake bayyana damuwarta kan batan mijinta a wata hira ta bidiyo da jakada mai jiran gado, Reno Omokri, wanda ya wallafa hirar a shafinsa na Facebook.
Omokri ya kai ziyara gidansu inda ya yi alkawarin tabbatar da adalci da tallafa wa Khadija da ‘ya’yanta biyu.
Da aka tambaye ta abin da take fata bayan shekaru da suka shude, Kadijah ta ce:
“Muna addu’a wata rana zai dawo.”

Source: Twitter
Ta roki ‘yan Najeriya da su taimaka domin a san halin da mijinta yake ciki, ko yana raye ko kuwa akasin haka.
Khadijah ta kuma tuna wani tsohon sako da aka wallafa a 2019 inda 'dan tsohon gwamnan Kaduna ya ke cewa Dadiyata yana yada karya.
Ta ce wani ne ya nuna mata sakon domin a lokacin ba ta da waya, inda ta bayyana cewa lamarin ya yi mata ciwo.
“Na ji zafin abin sosai, ba zan iya bayyana yadda na ji ba."
Ta ce ta ga lokacin da aka sace mijinta daga taga, yayin da yake sauka daga motarsa a cikin harabar gidansu a ranar 2 ga Agustan 2019.
Ana mayar da magana kan bacewar Dadiyata
Lamarin ya sake daukar hankali a ranar 14 ga Fabrairu, 2026 lokacin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta duk wata alaka da batun sace Dadiyata.
El-Rufai ya ce Dadiyata ya fi sukar gwamnatin Kano fiye da ta Kaduna, yana mai cewa bai ma san shi ba sai bayan iyalansa sun kai rahoto ga ‘yan sanda.
A martaninsa, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya musanta zargin da ake masa ta bakin tsohon kwamishinansa na yada labarai.
Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa zargin ba shi da tushe kuma ana kokarin kauce wa abin da ya faru a Kaduna ne kawai.
A rahoton jaridar, ta bayyana cewa jami'an DSS na shirin gayyatar 'ya'yan Nasir El-Rufa'i a kan lamarin domin amsa tambayoyi.
Daga cikin 'ya 'yan El-Rufai da suka yi fice a kafofin sada zumunta akwai Honarabul Bello El-Rufai wanda aikin majalisa ya dauke masa hankali da kuma Bashir El-Rufai.
Sai bai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ba ta bayyana komai a kan shirin gayyatar yaran El-Rufa'i ba.
Abba ya yi magana kan sace Dadiyata
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi alkawari ba bin diddigi domin a gano saihin zance kan zagin sace Abubajar Idirs da aka fi sani da Dadiyata a jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kano ya ce za su hada-kai da jami’an tsaro domin a gano wannan Bawan Allah da wasu mutane dauke da bindiga suka sace har gida a shekarar 2019.
Gwamnan ya ce har yau ba su manta da wannan Bawan Allah wanda masoyi ne kuma ‘dan tafiyar Kwankwasiyya wanda ya bace ba, za a yi kokari wajen gano shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


