An Yi Rashi a Najeriya: Farfesa Jeyifo, Shugaban Kungiyar ASUU na Farko Ya Mutu

An Yi Rashi a Najeriya: Farfesa Jeyifo, Shugaban Kungiyar ASUU na Farko Ya Mutu

  • Farfesa Biodun Jeyifo ya mutu yana da shekaru 80 a duniya sakamakon matsalar rashin lafiyar koda a birnin Legas a yau Laraba
  • An ce fitaccen masanin ne shugaban kungiyar malaman jami'o'i ta Nijeriya wato ASUU na farko, kuma ya koyar a fitattun jami'o'in duniya
  • Farfesa BJ ya bar yara guda uku wadanda duka suka yi fice a fannonin ilimin kimiya da zane da kuma taimakon jama'a a kasa da kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Najeriya ta yi rashin babban masanin ilimi kuma mai sharhi kan adabi, Farfesa Biodun Jeyifo, wanda aka fi sani da "BJ" a fadin duniya.

Farfesa Jeyifo ya rasu ne a yau Laraba sakamakon lalacewar koda a birnin Legas, wata daya da kwanaki biyar kacal bayan ya cika shekaru 80 a duniya.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Fitaccen masanin ilimi kuma mai sharhi kan adabi, Farfesa Biodun Jeyifo ya mutu
Farfesa Biodun Jeyifo (farko daga hagu) yana sauraron laccoci da aka gudanar a taron bikin cikarsa shekara 80. Hoto: Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism
Source: Facebook

Farfesa Biodun Jeyifo ya mutu

Jaridar PM News ta rahoto cewa an haifi wannan babban malami a birnin Ibadan a ranar 5 ga Janairu, 1946, inda ya gudanar da dukkan karatunsa na farko a can.

Rahoton ya nuna cewa Farfesa Jeyifo ya yi ilimi da kuma rayuwarsa ne a birnin Ibadan wanda ya kasance matattarar ilimi da al'adu a lokacin da yake matashi.

Marigayi Farfesa BJ ya kasance mutum na uku da ya taba samun digiri na farko mai daraja ta daya (first-class) a fannin Turanci a Ibadan.

Gwagwarmaya da kuma aikin koyarwa

Farfesa Biodun Jeyifo ne shugaban farko na kungiyar malaman jami'o'i ta kasar nan (ASUU) a lokacin da yake koyarwa a jami'ar Ife.

Ya sadaukar da rayuwarsa wajen fafutukar kwato hakkin malaman jami'a da kuma inganta tsarin ilimin gaba da sakandare a cikin kasar Najeriya.

Ya koyar a jami'o'in Cornell da Harvard dake kasar Amurka, inda ya yi ritaya a shekarar 2019, kamar yadda wani rahoto da aka wallafa a shafin WikiPedia ya nuna.

Kara karanta wannan

Ana wata sai ga wata: 'Yan bindiga sun sake kai hari coci, sun sace masu ibada

Farfesa Jeyifo ya kasance babban mai ra'ayin gurguzu wanda ya yi amfani da iliminsa wajen fafutukar adalci ga dukkanin talakawan duniya.

Fitaccen masanin ilimin bai tsaya kawai ga karatun littattafai ba, ya yi amfani da hikimarsa wajen horar da matasa da sauran malaman jami'a masu tasowa.

Farfesa Biodun Jeyifo shi ne shugaban kungiyar ASUU na farko a Najeriya.
Farfesa Biodun Jeyifo ya na jawabi a taron cikarsa shekaru 80 da haihuwa. Hoto: Folorunso Fatai Adisa
Source: Facebook

Iyalan da Farfesa Jeyifo ya bari

Farfesa Jeyifo ya bar yara guda uku wadanda kowannensu ya yi suna a fannonin ilimi daban-daban a kasar Amurka da sauran wurare, in ji rahoton Premium Times.

Dansa na farko, Okunola Bamidele, masanin kwakwalwa ne, yayin da Olalekan Babajide ya kasance fitaccen mai zane da gine-gine a birnin Brooklyn.

Yarsa Ruth Ayoka tana karatun digiri a jami'ar Cornell inda take taimaka wa marasa galihu da kuma wadanda aka ci zarafi a gida.

Daukacin jami'o'in da ya yi aiki a cikinsu suna ci gaba da aika sakonnin ta'aziyya ga iyalansa da kuma dalibansa dake fadin duniya.

ASUU ta cimma yarjejeniyar da gwamnati

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya sun cimma matsaya kan sabunta yarjejeniyar shekarar 2009.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Matar Aure, Khadija Jamilu ta dabawa mijinta wuka a mazakuta

Rahoto ya ce sabuwar yarjejeniyar ta tanadi karin albashi ga malamai, inganta tsarin fansho da sabon tsarin tallafin jami’o’in gwamnati.

An tsara fara aiwatar da yarjejeniyar ne daga 1, Janairu, 2026, tare da bukatar ASUU ga gwamnati ta cika dukkan alkawuran da aka dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com