Matashi ya yi farin cikin kammala Digiri bayan shekara 10 ya na fafatawa a ABU Zaria

Matashi ya yi farin cikin kammala Digiri bayan shekara 10 ya na fafatawa a ABU Zaria

  • Abba Abubakar Santalee ya fito dandalin Twitter yana murnar kare digirin B. Pharm a jami’ar ABU Zaria
  • Pharm. Abba Abubakar Santalee ya iya kammala karatunsa bayan shekara goma yana gwabzawa
  • Ciroman na garin Tsakuwa ya ba mutane shawarar ka da su karaya kamar yadda bai cire rai a jami’a ba

Kaduna - Wani Bawan Allah mai suna Abba Abubakar Santalee ya bayyana farin cikinsa yayin da ya kammala karatun digirin farko a jami’ar ABU Zaria.

Legit.ng Hausa ta fahimci Abba Abubakar Santalee ya fito ya bayyana wannan abin alheri ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu 2022.

Inda farin cikin Pharm. Abba Abubakar Santalee yake shi ne, ya dauki lokaci mai tsawo kafin samun takardar shaidar Digiri a wannan babbar jami’a.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari Ya Shiga Jerin Masu Takarar Gwamna a Jiharsa

Da yake bayanin abin da ya sa ya dade bai gama karatun ba, Abba Abubakar Santalee ya ce yajin-aikin kungiyar ASUU ya bata masa akalla shekara daya.

Haka zalika Abba Santalee ya gamu da kalubale a jami’ar ta Ahmadu Bello da ke gari Zaria, har ta kai ya kara shekaru uku kafin ya ci duka jarrabawansa.

A tsawon shekara goma da ya yi yana karatu ne kuma Ubangiji ya jarabci Abba Santalee da annobar COVID-19 wanda ta jawo aka rufe duk makarantu.

Matashin ABU Zaria
Abba Abubakar Santalee Hoto: @Malam_Santalee
Asali: Twitter

An dade ana abu daya

Tun shekarar 2012 Santalee da sauran abokan karantunsa suka samu shiga jami’ar. Amma bai yi sallama da makarantar ba sai a watan Afrilun shekarar nan.

Mun tuntubi wasu wadanda suka yi karatu a sashen koyar da ilmin hada magunguna a wannan jami’a, inda mu ka fahimci digiri a fannin sai wanda ya dage.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Najeriya na matukar bukatar na mulke ta saboda wasu dalilai da ke kasa

Wata ta shaidawa Legit.ng Hausa cewa Santalee yana gaban ta a aji, amma ta kammala aikin sharar fage, yanzu haka ta na daf da gama yi wa kasa hidima.

Saboda yajin-aikin da kungiyar ASUU ta ke yi, mu na da labarin cewa sai dai a ma’aikatar NITT da ke Basawa ne aka iya shirya bikin yaye wadannan daliban.

Siyasa da sarauta

Baya ga karatu, Pharm. Abba Santalee ya hada da siyasa, har ta kai ya yi takarar shugaban kungiyar daliban jihar Kano ta NAKSS na reshen ABU a 2017.

A ranar 26 ga watan Maris 2022 mu ka ji labarin an ba shi sarautar Ciroman Tsakuwa a kauyensu. Bayan ‘yan kwanaki ya zama malamin magunguna mai lasisi.

Pharm. Abba Abubakar Santalee a Twitter

“Karatun shekaru biyar, aka hada da karin shekaru uku, da yajin-aikin ASUU na shekara daya…da kuma tsawon shekara daya a lokacin annobar COVID-19…”
“…Yanzu an karkare Digiri a cikin shekaru goma. A yau na zama malamin magunguna! Na tsira…Ka da ka taba cire tsammani.” - Pharm. Abba A. Santalee

Kara karanta wannan

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel