Matsalolin da Za a Iya Fuskanta a Hajjin Bana bayan Sheikh Pakistan Ya Yi Murabus

Matsalolin da Za a Iya Fuskanta a Hajjin Bana bayan Sheikh Pakistan Ya Yi Murabus

  • Masu gudanar da aikin Hajji sun nuna damuwa kan sauyin shugabanci a hukumar NAHCON gab da fara aikin Hajjin shekarar nan
  • Sun ce murabus din shugaban NAHCON na iya kawo cikas ga shirye-shiryen da aka kusa kammalawa wanda na daf da zuwa karshe
  • Kungiyar ta roki Gwamnatin Tarayya ta bari a kammala shirye-shiryen domin gudun tangarda a aikin Hajjin bana ta 1447

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Masu shirya aikin Hajji karkashin kungiyar 'Association of Hajj and Umrah Operators (Northcentral) Nigeria' sun magantu kan aikin hajjin bana.

Kungiyar ta nuna damuwa kan murabus din shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman inda ta ce hakan ka iya shafar aikin Hajjin 2026.

Ana fargabar samun matsala bayan murabus din Sheikh Pakistan
Shugaban hukumar NAHCON, Abdullahi Sale Usman. Hoto: Jibwis Nigeria.
Source: Facebook

Shugaban kungiyar, Mallam Samsudeen Abdulsalam, shi ya bayyana haka a wata sanarwa kamar yadda The Nation ta tattabar.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Dalilin murabus din Sheikh Abdullahi Pakistan

Hakan ya biyo bayan murabus din Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan wanda ya jawo maganganu kan shugabancin hukumar.

Malamin daga bisani ya bayyana dalilin da ya sa ya yi murabus yana mai karyata cewa ya yi ne bayan taso shi a gaba ko wata matsala a hukumar.

Ya yi godiya na musamman ga Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran masu ruwa da tsaki a hukumar.

Ana fargaba bayan murabus din Sheikh Pakistan

Samsudeen Abdulsalam ya ce murabus din da aka yi a wannan lokaci mai muhimmanci ya haifar da tambayoyi kan shirye-shiryen da aka kusa kammalawa domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Ya ce a farkon watan nan Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabia, ya ziyarci Najeriya domin wayar da kan masu aikin Hajji, inda ya ce Hajjin da ya gabata na daga cikin mafi muni ga ’yan Najeriya.

Ya ce ministan ya bukaci a kara kaimi wajen shiri domin aikin Hajjin 2026 ya fi na baya kyau, tare da yin gargadin cewa duk wata tangarda na iya janyo matsala ga mahajjatan Najeriya.

Kara karanta wannan

NAHCON: Bayan murabus din Pakistan, an gano yadda Shettima ya sauya tunanin Saudiyya

Yadda ake zargin samun matsala a hajjin bayan murabsu din Sheikh Pakistan
Maniyyata na shirin hawa jirgi domin tafiya Hajji a kasa mai tsarki. Hoto:NAHCON.
Source: Facebook

'Yadda shirin hajjin bana zai iya wargajewa'

Kungiyar ta ce abin damuwa ne yadda aka yi sauyin shugabanci a daidai lokacin da aka riga aka kulla yarjejeniyoyi da kamfanonin jiragen sama, inda aka tsara fara jigilar farko ranar 1 ga Mayu, 2026.

Haka kuma, an kusa kammala loda bayanan mahajjata, an riga an ware masauki da tantuna yayin da ake sa ran kammala batun biza a mako mai zuwa.

Kungiyar ta roki Gwamnatin Tarayya da ta bari shugabannin da suka fara shirye-shiryen su kammala aikin domin tabbatar da an gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.

Saudiyya ta kara wa'adin cike bayanan maniyyata

Mun ba ku rahoton cewa hukumomi a Saudiyya sun kara wa Najeriya lokaci domin kammala shigar da bayanan maniyyata aikin Hajjin 2026 a dandalin Nusuk Masar.

Karin lokacin ya zo ne bayan sa hannun gwamnatin tarayya, bisa umarnin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Hukumar NAHCON ta gargadi masu shirya Hajji da su yi gaggawa, domin wannan karin lokaci na kwanaki ne kacal.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.