Tsohuwar Ministar Jonathan Ta Bayyana a Kotun Ingila kan Zargin Badakalar Miliyoyi

Tsohuwar Ministar Jonathan Ta Bayyana a Kotun Ingila kan Zargin Badakalar Miliyoyi

  • Diezani Alison-Madueke, tsohuwar Ministar mai a Najeriya, ta bayyana a gaban kotun Southwark a Landan kan tuhumar cin hanci na £100,000
  • Ana shirin fara cikakken shari’arta ranar 26 ga Janairu, 2026, bayan sauraron gabatarwar farko a tuhumar da ake yi wa Madueke na badakala
  • Tsohuwar ministar mai shekaru 65 ta musanta tuhuma shida da ake yi mata, yayin da aka ce ta amfana da kudi da abubuwa masu yawa na haramun a gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohuwar Ministar Albarkatun Mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana a gaban Southwark Crown Court da ke London, Birtaniya.

Ta gurfana a kotun ne domin sauraron gabatarwar farko na shari’arta da ake yi bisa tuhumar cin hanci na fam 100,000.

Kara karanta wannan

An cafke babban malamin Musulunci, an kai shi kotu kan cinye filaye a Kano

An gurfanar da Alison Madueke a gaban kotun Ingila
Mace ta farko da ta zama Ministar mai a Najeriya Hotto: Willy Ibimina Jim-george
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Diezani, wacce ta rike mukamin minista daga shekarar 2010 zuwa 2015, ita ce mace ta farko a matsayin minista a fannin mai a Najeriya da kuma mata ta farko da ta shugabanci kungiyar OPEC ta duniya.

Diezani Madueke ta bayyana a kotun Landan

Daily Post ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa an tsara shari’ar a gaban Alkali Thornton a ranar Litinin, a Kotun 8.

An yi gabatarwar farko domin shirya cikakken shari’a wanda aka tsara zai fara ranar 26 ga Janairu, 2026. Wannan mataki ya hada da tattaunawar fasaha da zaɓen masu zartar da hukunci, inda Diezani ta halarci kotu.

Diezani Alison Madueke ta karyata dukkanin zargin da ake mata
Tsohuwar Minista mai a Najeriya, Alison Madueke Hoto: Getty
Source: Getty Images

Tsohuwar minista mai shekaru 65 ta kasance a kan beli tun lokacin da aka kama ta a Landan a watan Oktoba na shekarar 2015. Ta musanta dukkannin tuhuma guda shida da aka yi mata.

Hukumar National Crime Agency (NCA) ta Birtaniya ce ta kai karar Diezani a shekarar 2023, inda ta ce ta aikata laifuffukan karɓar cin hanci tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun canja zance kan zargin sace masu ibada 160 a Kaduna

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Madueke

Hukumar NCA ta bayyana cewa Diezani ta amfana da aƙalla fam £100,000 tsurar kuɗi, motocin masu direbobin da ke tuƙa ta da jiragen sama masu zaman kansu, da gidaje da yawa a Landan.

Hakanan an bayyana wasu abubuwa na kudi, daga ciki har da kayan daki, gyare-gyaren gidaje, ma’aikata don kula da gidajen, biyan kudin makaranta masu zaman kansu, da kyaututtuka daga manyan shagunan kayan alatu kamar Louis Vuitton.

Bayan Diezani, akwai wasu mutane biyu da ake tuhumarsu a wannan shari’a: Doye Agama, wanda ya bayyana ta hanyar bidiyo a kotu, da Olatimbo Ayinde, wanda ya kasance a gaban kotu a zahiri.

An yi hasashen shari’ar za ta dauki mako 10 zuwa 12 kafin a kammala shari'ar da ake zargin Madueke na karban na goro.

EFCC ta yi gwanjon kayan Madueke

A baya, mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi kira ga mutane da kamfanoni su nemi sayen kayan da gwamnatin tarayya ta karbe daga hannun wadanda ake zargi da aikata ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun mika bukata ga kotu game da garkame Abubakar Malami SAN

Wannan mataki na EFCC na daga cikin dabarun tabbatar da cewa kadarorin da aka karbe daga hannun masu aikata laifi ba su tsaya a banza ba, kuma an basu dama ga masu sha’awa su siya bisa doka.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta na tuhumar Diezani Alison-Madueke da mallakar wadannan kaya ta haramtacciyar hanya, inda aka sa wasu daga cikin kadarorinta a kasuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng