EFCC: Yajin-aikin Ma’aikatan shari’a ya jawo cikas wajen binciken Diezani Madueke

EFCC: Yajin-aikin Ma’aikatan shari’a ya jawo cikas wajen binciken Diezani Madueke

- Har gobe hukumar EFCC ta na shari’a da Diezani Alison-Madueke a kotu

- Ana zargin tsohuwar Ministar da wawurar kudi lokacin da ta ke gwamnati

- Yajin-aikin ma’aikatan shari’a ne ya jawo aka kara dakatar da shari’ar jiya

Yajin-aikin da ma’aikatan bangaren shari’a suke yi, ya sa an gaza sauraron karar hukumar EFCC da tsohuwar Ministar harkar mai, Diezani Alison-Madueke.

A ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2021, aka shirya cewa za a shiga kotu da Madam Diezani Alison-Madueke, Amma a karshe hakan ba ta yiwu a jiyan ba.

Yajin-aikin da kungiyar JUSUN ta ma’aikatan shari’a suke yi, ya cika makonni bakwai a yau.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun shiga kotu, sun dauke Alkali a Katsina

Shari’ar Alison-Madueke da gwamnatin Najeriya ta zo gaban Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya na Abuja, Ijeoma Ojukwu, a ranar 3 ga watan Maris.

A lokacin da aka soma zaman wannan shari’a, ba a san cewa malaman shari’a za su tafi yajin-aiki ba, don haka aka sa rana, za a cigaba da sauraron karar a Mayu.

Alkali mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ba hukumar EFCC daga yanzu zuwa ranar 17 ga watan Mayu, 2021, ta bayyana domin ta yi wa kotu bayanin inda aka kwana.

Kotu ta nemi jin kokarin da EFCC ta ke yi wajen ganin sun gabatar da tsohuwar Ministar tarayyar a gaban Alkali, yanzu haka wanda ake tuhuma ta fake a Birtaniya.

EFCC: Yajin-aikin Ma’aikatan shari’a ya jawo cikas wajen binciken Diezani Madueke
Diezani Alison-Madueke Hoto: www.bbc.com/pidgin/52954208
Asali: UGC

KU KARANTA: An fito da sunayen wadanda suke neman kujerar Shugaban PDP

Daga shari’ar da aka yi zuwa wannan rana ya na cikin jerin kalulabalen da EFCC ta fuskanta a wannan shari’a da aka soma bayan APC ta karbi gwamnati a 2015.

Tun a Nuwamban 2018, EFCC ta gabatar da zargin aikata laifuffuka 13 kotu. Sai dai har yanzu Alkali ba ta kai ga yanke hukunci a wannan doguwar shari’a ba.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya tabbatar da cewa ba su manta da batun Diezani Alison-Madueke ba, ya ce kuma an karbe wasu dukiyoyi daga hannunsa.

Dazu kun ji cewa an yi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan raddi, an tuna masa abin da ya yi wa tsohon gwamnan babban banki, Sanusi Lamido Sanusi.

Har ila yau, an tuna masa cewa a lokacin mulkinsa ne aka tsige Gwamna Murtala Nyako daga kan mulki, sannan aka turke gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel