An Kama Wani Ɗan Najeriya Ɗauke da Sassan Ɗan Adam, Ƴan Sanda Sun Ɗauki Mataki
- 'Yan sanda sun gano kwarangwal din mutum a boye cikin jan kyalle a motar Kazeem Ayegbo dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan
- Rundunar ta ce za ta fadada bincike har zuwa wajen jihar Oyo don kamo wadanda ke da hannu a safarar sassan dan Adam din
- Wannan na zuwa ne bayan an kama Lawal Ibrahim, wanda ake zargin ya kashe abokin aikinsa ta hanyar daba masa kwalba a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Jami’an rundunar 'yan sanda dake kan titin Legas zuwa Ibadan a jihar Oyo, sun gano wani jan kyalle dauke da kwarangwal da wasu abubuwa da ake zargin sassan jikin mutum ne.
Kakakin rundunar yan sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2025 a birnin Ibadan.

Source: Twitter
An kama direba da sassan dan Adam
A cewar sanarwar, an gano wadannan kwarangwal ne a boye cikin kayan fasinjoji yayin da jami'ai suke gudanar da aikin binciken ababen hawa, in ji rahoton TVC News.
Jami'an yan sandan sun kama direban motar mai suna Kazeem Ayegbo, wanda yake tafiya daga Legas zuwa Osogbo, a daidai kauyen Guru Maharaji dake kan babbar hanyar.
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano wani jan kyalle dauke da kwarangwal da sauran abubuwa da ake zargin sassan gawar mutum ne."
Osifeso ya kara da cewa an riga an fara gudanar da bincike mai zurfi domin gano asali da kuma manufar mallakar kwarangwal din mutum da aka gano a cikin motar tasa.
Fadada bincike zuwa wasu jihohin
Rundunar ta bayyana cewa binciken zai fadada har zuwa wajen Jihar Oyo domin gano dukkan mutanen da suke da hannu a cikin wannan lamari.

Kara karanta wannan
Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai a Borno, mutane fiye da 40 sun mutu
Jami'an tsaro sun tabbatar wa mazauna jihar cewa za a tura wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
Kazalika, rundunar ta bukaci jama'a da su ci gaba da ba su hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Source: Original
An kashe mutum a wurin ginin gida
Wannan na zuwa ne bayan 'yan sandan sun tabbatar da kisan wani matashi mai shekaru 18 mai suna Raimi Ige, a wani wurin ginin gida dake yankin Iyana-Ajia, in ji rahoton Punch.
Bincike ya nuna cewa rashin jituwa tsakanin wasu leburori biyu ne ya rikide zuwa fada, inda Lawal Ibrahim mai shekaru 22 ya daba wa Raimi kwalba.
Raimi ya rasu ne yayin da ake garzaya da shi asibiti, kuma yanzu haka an ajiye gawar tasa a dakin adana gawarwaki na asibitin Adeoyo domin bincike.
Yiwuwar samuwar kasuwar sassan dan Adam
A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan Filato ta yi bayani kan yiwuwar samuwar wata kasuwa da ake sayar da sassan jikin mutum a jihar.
Kakakin ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa kisan gilla da ake domin yin tsafe-tsafe da zai sanya samun irin kasuwar ya yi matukar kadan a Filato.
Wani malamin addinin Kirista, Fasto Polycarp Lubo ya bukaci iyaye su hana ‘ya’yansu shiga kungiyoyin asiri da damfara domin samar da zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

