Tsoron-Allah-a-zuci: An kama wani ustazu da abokan sa da kwarangwal din mutum a Ogun

Tsoron-Allah-a-zuci: An kama wani ustazu da abokan sa da kwarangwal din mutum a Ogun

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Ogun dake a kudu maso yammacin Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke wani ustazu dake ikirarin zama malamin islama mai suna Jami'u Olasheu tare da abokan sa uku da kan mutum.

Kamar yadda muka samu, Jami'u Olasheu mai shekaru akalla 35 a duniya tare da abokan nasa an kama su ne yayin wani sintiri na jami'an 'yan sandan a cikin satin da ya gabata a unguwar Kofedoti, karamar hukumar Agbara.

Tsoron-Allah-a-zuci: An kama wani ustazu da abokan sa da kwarangwal din mutum a Ogun

Tsoron-Allah-a-zuci: An kama wani ustazu da abokan sa da kwarangwal din mutum a Ogun
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Hotuna da labarin wata mata da tsutsa ke fita daga jikin ta kullum

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa sauran abokan ustazun da aka kama tare da shi sun hada da Teslim Ayeniromo, mai shekaru 45, da kuma Sunday Kolade, mai shekaru 35 a duniya.

Da yake karin haske game da batun, jami'in hulda da jama'a na rundunar, Abinbola Oyeyemi ya bayyana cewa tabbas jami'an su ne suka kama mutanen kuma tuni an soma tatsar bayanai daga wurin su da zai taimaka wajen kama sauran masu laifin.

Masu sharhi akan harkokin yau da kullum dai kan zargi irin ayyukan assha din nan dake da alaka da tsafe-tsafe kan yi tashin gwowron zabi musamman idan kakar zabe ta soma kankama kusan ko wane lokaci a tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel