JAMB Za Ta Fara Sayar da Fom din Jarabawar UTME 2026, Ta Kafa Sharuda ga Dalibai

JAMB Za Ta Fara Sayar da Fom din Jarabawar UTME 2026, Ta Kafa Sharuda ga Dalibai

  • Hukumar JAMB ta sanar da shirin sayar da fom din jarrabawar UTME ta shekarar 2026 inda ta sanya ranar 26 ga Janairu 2026 don fara rajista
  • Daliban da ba su kai shekara 16 ba kafin watan Satumba ba za su samu damar zana jarrabawar ba sai idan sunada hazaka ta musamman
  • JAMB ta kuma bayyana cewa ta kasa kudin rajista zuwa kashi uku yayin da ta bayyana ranar da za a zana jarabawar a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta ƙasa (JAMB), ta sanar da fara sayar da fom din jarrabawar UTME da DE na shekarar 2026/2027.

Wannan sanarwa ta fito ne ta hannun shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, wanda ya fayyace cewa an tsara ranakun da dabarun gudanar da jarrabawar domin tabbatar da tsabtar tsarin ilimi a Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Fitacciyar mawakiyar yabon addini ta riga mu gidan gaskiya

JAMB ta sanya ranar fara rajistar jarabawar UTME 2026
Wasu dalibai suna layin rajistar jarabawa da tambarin hukumar JAMB. Hoto: JAMB HQ Updates
Source: Facebook

JAMB ta tsaurara matakai kan shekarun jarrabawa

Babban sauyin da aka samu a wannan shekarar shi ne tsaurara matakan shekaru ga masu son yin jarrabawar, kamar yadda JAMB ta sanar a shafinta na X.

JAMB ta sanar da cewa:

“Duk ɗalibin da shekarunsa ba su kai 16 ba kafin ranar 30 ga watan Satumba, 2026, ba zai samu damar yin rajista ba.”

Sai dai, hukumar ta samar da wata dama ta musamman ga yara masu ƙananan shekaru amma masu hazaka.

Muddin ɗalibi ya ci kashi 80 a dukkan jarrabawowinsa na SSCE, UTME, da sauran tantancewa, hukumar za ta duba yiwuwar ba shi rangwame bayan an yi masa tantancewa ta musamman.

Jadawalin ranakun rajistar JAMB 2026

JAMB ta fitar da ranaku daban-daban domin sayar da fom din jarabawar UTME kamar haka:

  • Sayar da E-PIN: Za a fara ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026, sannan a rufe ranar 26 ga Fabrairu, 2026.
  • Rajistar UTME: Za a buɗe shafin rajista ranar 26 ga Janairu, 2026, sannan a rufe ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
  • Rajistar DE: Wannan zai fara ne daga ranar 2 ga Maris zuwa 25 ga Afrilu, 2026, kuma a ofisoshin JAMB na jihohi ne kawai za a yi.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

Game da kuɗin rajista kuwa, hukumar ta karkasa su zuwa gida uku domin ba ɗalibai zaɓi:

  1. Direct Entry (DE): ₦5,700.
  2. UTME ba tare da jarabawar gwaji (mock) ba: ₦7,200.
  3. UTME tare da jarabawar gwaji (mock): ₦8,700.
Hukumar JAMB ta ce 'yan kasa da 16 years ba za su zana jarabawa ba sai idan suna da hazaka ta musamman.
Shugaban hukumar JAMB Ishaq Oloyede ya na zaune a ofishinsa da ke Abuja. Hoto: @JAMBHQ
Source: Facebook

Ranakun gudanar da jarrabawar UTME 2026

Hukumar ta sanya Asabar, 28 ga Maris, 2026, a matsayin ranar gudanar da jarrabawar gwaji (Mock-UTME) ga ɗaliban da suka biya kuɗin hakan.

Ita kuwa babbar jarrabawar UTME ta shekarar 2026 baki ɗaya, za ta kankama ne daga ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026, zuwa ranar Asabar, 25 ga Afrilu, 2026.

Farfesa Oloyede ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta lamunci kowane nau'i na zamba ko kuskure daga cibiyoyin CBT ba.

An buƙaci ɗalibai su tabbatar sun shigar da bayanansu daidai domin kauce wa matsalar tantancewa ta amfani da yatsu a ranar jarrabawa.

Dalilin faduwar dalibai JAMB 2025

A wani labari, mun ruwaito cewa, sama da dalibai miliyan ɗaya da rabi sun kasa samun maki 200 a jarabawar UTME 2025 sakamakon kura-kuran da JAMB ta samu.

Kara karanta wannan

Mutum 2 da za su gabatar da shaida a shari'ar Ganduje sun fara fuskantar hadari a Kano

Farfesa Ishaq Oloyede ya ɗauki alhakin matsalar, yana mai cewa sakaci daga hukumar JAMB ne ya haddasa wannan mummunan sakamako.

JAMB ta sanar da cewa sama da dalibai 380,000 za su sake zana jarabawar, sannan ta hada kai da ƙwararru domin duba matsalolin da aka fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com