An Shirya Jana'izar Abokan Anthony Joshua da Suka Rasu a Hatsari a Masallacin London

An Shirya Jana'izar Abokan Anthony Joshua da Suka Rasu a Hatsari a Masallacin London

  • Hukumomi sun tabbatar da shirya sallar jana'izar abokan dan wasan dambe, Anthony Joshua a wani masallaci a London
  • Za a yi sallar jana’izar mutanen biyu da suka rasa rayukansu yayin hatsarin mota a Najeriya a gobe Lahadi, 4 ga Janairu 2026
  • Anthony Joshua ya tsira da ƙananan raunuka, yayin da abokansa biyu suka mutu a hatsarin wanda ya tayar da hankula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

London, UK - An shirya gudanar da sallar jana’izar abokan shahararren dan dambe a Najeriya, Anthony Joshua bayan hatsarin mota.

Wadanda suka rasu a hatsarin sun hada da Sina Ghami da Abdul Latif “Latz” Ayodele lamarin da ya tayar da hankula.

An shirya jana'izar abokan Joshua a masallacin London
Anthony Joshua da abokansa, Abdul Lateef “Latz” da Sina “Evolve” Ghami. Hoto: @sodyOka4.
Source: Twitter

An shirya jana'izar abokan Anthony Joshua

Rahoton Leadership ya ce an shirya yi musu sallar jana'iza a babban masallacin birnin London ranar Lahadi, 4 ga Janairu 2026.

Kara karanta wannan

Tsohon dan majalisa da aka sace a masallaci ya samu 'yanci bayan biyan N50m

Majiyoyi sun nuna cewa an mayar da gawarwakin mutanen biyu Birtaniya ne bayan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyyar rasuwarsu a Najeriya.

Za a fara sallar jana’izar da misalin ƙarfe 10:00 na safe a babban masallacin London da ke lamba 146 a kan hanyar Park da ke London.

Wata sanarwa daga kamfanin 'Boxing King Media' da aka fitar a ranar Asabar ta tabbatar da shirye-shiryen jana’izar, inda ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalai da masoyan marigayan.

Anthony Joshua ya gamu da hatsarin mota
Dan wasan dambe a Birtaniya, Anthony Joshua. Hoto: Megan Briggs.
Source: Getty Images

Yadda hatsarin mota ya hallaka abokan Joshua

Sina Ghami, wanda ya dade yana horar da Anthony Joshua a bangaren kara ƙarfi da motsa jiki, da kuma Abdul Latif Ayodele, mai horas da shi kai tsaye, sun rasu ne a hatsarin mota da ya faru ranar 29 ga Disamba, 2025.

Rahotanni sun ce Anthony Joshua ma yana cikin motar Lexus SUV da ta yi hatsari da wata babbar mota da ke tsaye a kan titin Lagos–Ibadan, a yankin Makun da ke Jihar Ogun, amma ya tsira da ƙananan raunuka.

An ce jana’izar da za a yi a London za ta bai wa iyalai, abokai da kuma ‘yan damben duniya damar yi wa marigayan bankwana na ƙarshe, ganin irin rawar da suka taka a rayuwa da nasarar Anthony Joshua.

Kara karanta wannan

Jirgin saman sojoji ya yi hatsari a kokarin yaki da 'yan ta'adda a Niger

Wani wakilin 'Boxing King Media' ya bayyana cewa Sina Ghami da Latz Ayodele ba kawai abokan aiki ba ne ga Anthony Joshua, illa iyali ne a gare shi, cewar Vanguard.

Ya bayyana cewa jajircewarsu, ƙwazo da zumunci ba za su taɓa gushewa daga tarihi ba duba da irin gudunmawar da suka ba rayuwarsa gaba daya.

Anthony Joshua ya doke abokin karawarsa

A baya, an ji cewa damben Anthony Joshua da Francis Ngannou a birnin Riyadh da ke kasar Saudi Arabiya ya dauki hankalin mutane a duniya.

Drake ya sa kudi yana jiran Joshua ya ji kunya, amma damben bai yi wani tsawo ba sai gwarzon ya doke abokin karawarsa.

Aubrey Drake Graham ya sa $615, 000 da aka cinye a cacar, a lissafin kudin Najeriya a wancan lokaci watau 2024, ya rasa fiye da N980m kenan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.