Mawaki Yayi Asarar Kusan Naira Biliyan 1 da Anthony Joshua Ya Doke Nnagano a Dambe

Mawaki Yayi Asarar Kusan Naira Biliyan 1 da Anthony Joshua Ya Doke Nnagano a Dambe

  • Damben Anthony Joshua da Francis Ngannou a birnin Riyadh da ke kasar Saudi Arabiya ya dauki hankalin mutane a duniya
  • Drake ya sa kudi yana jiran Joshua ya ji kunya, amma damben bai yi wani tsawo ba sai gwarzon ya doke abokin karawarsa
  • Aubrey Drake Graham ya sa $615, 000 da aka cinye a cacar, a lissafin kudin Najeriya a yau, ya rasa fiye da N980m kenan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Riyadh - Fitaccen mawakin nan Aubrey Drake Graham wanda aka fi sani da Drake ya yi asarar dalolinsa wajen cacar wasan dambe.

Drake ya sa kudi a damben da Anthony Joshua ya yi da Francis Ngannou a kasar Saudiyya kamar yadda tashar Sky ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Kudin siminti ya ragu zuwa N7,800": 'Dan kasuwa ya kira kwastama, ya maida masa ragin N400

Anthony Joshua da Francis Ngannou
Drake ya rasa kudi a damben Anthony Joshua da Francis Ngannou Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ngannou ya sha kashi hannun Anthony Joshua

Mawakin na kasar Kanada ya sa fam $615,000 da sa ran Ngannou zai doke Anthony Joshua, amma ba hakan ya faru jiya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anthony Joshua wanda yana da alaka da Najeriya ya nunawa duniya karfinsa a jiya, ya samu nasara ne tun a zagaye na biyu.

Drake ya yi asara a wasan AJ v Ngannou

Da a ce Joshua ya sha kashi a damben, jaridar The Mirror ta ce Drake zai iya samun kusan $2m, watau Naira biliyan 3.1 kenan.

Tauraron ya saba samun kudi da caca a ‘yan shekarun bayan nan, ya kan sa kudi amma da alama yanzu ya rage samun sa’a.

Joshua ya ragargaji Ngannou a Saudi

Joshua ya yi abin da ya gagari Tyson Fury, ba a dade da fara damben ba ya yi wa Ngannou mummunan nushi da hannun dama.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

Abokin karawan na shi ya mike kuma aka cigaba da bugawa, amma bayan ‘yan mintuna gwarzon ya yi masa dukan da bai tashi ba.

NAN ta rahoto mawakin yana cewa caca tana da ban tsoro bayan ya rasa kudinsa a Riyadh, yana cikin attajiran masu waka a duniya.

Cacar Drake yau da sa'a gobe babu

A shekarar bara, Drake ya tashi da $1.3m a wani wasan dambe a sakamakon korar Dillon Danis da aka yi da ya kara da Logan Paul.

Kwanaki kuma Drake ya sa $920,000 yana mai fatan Israel Adesanya zai doke Sean Strickland, a karshe sai dai ya yi asarar kudinsa.

Yarima yana kawo sauyi a Saudiyya

A rahoton da aka fitar a baya, kun ji Saudiyya tana zuba biliyoyin kudi a harkokin wasanni domin kawo sauyi ga tattalin arzikinta.

Manyan taurari kamar Cristiano Ronaldo da Anthony Joshua suna neman fito da kasar ta yadda za ta samu farin jini a fadin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel